Kotu ta tsoma baki a takaddama kan dokar NCDC

Wata babbar kotun tarayya da ke zaman ta a Abuja ta umurci Majalisar Wakilai da ta dakatar da aikin da take yi a kan kudurin dokar cututtuka masu yaduwa wanda tuni ya tsallake karatu na biyu. A lokacin da take yanke hukuncin jiya Juma’a, Mai Shari’a Ifeoma Ojukwu ta kuma umarci Kakakin Majalisar Wakilan, Femi […]

Kotu ta tsoma baki a takaddama kan dokar NCDC

Mai Shari’a Ifeoma Ojukwu

Wata babbar kotun tarayya da ke zaman ta a Abuja ta umurci Majalisar Wakilai da ta dakatar da aikin da take yi a kan kudurin dokar cututtuka masu yaduwa wanda tuni ya tsallake karatu na biyu.

A lokacin da take yanke hukuncin jiya Juma’a, Mai Shari’a Ifeoma Ojukwu ta kuma umarci Kakakin Majalisar Wakilan, Femi Gbajabiamila, da Ministan Shari’a kuma babban lauyan gwamnati, Abubakar Malami, da Babban Sufeton ‘yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu, da kuma Akawun Majalisar Dokoki ta Kasa da su bayyana a gaban kotun.

“A takaice, wannan kotun tana sanar da wadanda ake kara a wannan shari’ar da su kasance cikin shiri”, inji mai shari’ar.

Mai Shari’a Ojukwu ta kara da cewa, “Muddin kuma wadanda aka yi sammaci suka gaza bayyana a gaban kotun kafin ranar da aka saka don zama na gaba, to tabbas kotu za ta tabbatar wa masu kara abin da suke bukata”.

Sanata Dino Melaye ne dai tun da farko ya shigar da karar a gaban kotun ta hannun lauyansa, Nkemakolam Okoro, yana neman a dakatar da ci gaba da karatun kudurin a zauren majalisar, yana zargin cewa kudurin na iya barazana ga ‘yancinsa in har ya kai ga zama doka.

‘Kudurin ya saba da Tsarin Mulki’

Saboda haka Melaye ya bukaci kotun da ta umurci wadanda yake kara da su cire sassa na 3(8), 5(3), 6, 8, 13,15, 16,17,19, 23, 30 da kuma na 47 na cikin kudurin dokar saboda sun ci karo da sashe na 33, da na 34, da na 35, da na 37, da na 38 da kuma na 40 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na shekara ta 1999.

Hakazalika, mai karar ya ce kudurin ya saba da tanade-tanaden yarjejeniyar ‘yancin dan-Adam ta Afirka da kuma wasu dokokin na Najeriya.

An dai gabatar da kudurin mai cike da ce-ce-ku-ce a zauren Majalisar karkashin jagorancin kakakinta, Femi Gbajabiamila a ranar 28 ga watan jiya kuma tuni kudurin ya wuce karatu na daya da na biyu.

Majalisar dai ta mayar da martani da kakkausar murya ga wani kira da Kungiyar Gwamnonin Najeriya ta yi da a dakatar da kudurin dokar, tana cewa ba ta gamsu da hanyar da gwamnonin suka bi don isar da sakonsu ba.

Kotun dai ta tsayar da 20 ga watan Mayu don ci gaba da sauraron karar.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos