Kotu ta dakatar da sabon Sarkin Kontagora
Kotun ta dage karar har zuwa ranar 20 ga watan Oktoban da muke ci.
Wata Babbar kotu da ke zamanta Minna a Jihar Neja, a ranar Talata, ta umarci Mohammed Barau Kontagora da ya daina kiran kansa a matsayin Sarkin Sudan na Kontagora.
Umarnin ya biyo bayan sauraron karar da wasu mutum 15 da ke neman kujerar suka gabatar a gaban kotun.
- Majalisar Malaman Kano ta dare kan sauke Sheikh Ibrahim Khalil
- Sarki Bamalli ya rushe Majalisar Masarautar Zazzau
Alkalin kotun, Abdullahi Mikailu ne ya yanke hukuncin bayan sauraron hujjojin da aka gabatar masa.
Kazalika, alkalin ya umarci Mohammed Barau Kontagora da ya daina kiran kansa a matsayin sarkin Kontagora na bakwai, har zuwa lokacin da za ta kammala shari’ar.
“Na ba da umarnin wucin gadi ga wanda ake kara da duk wani da ke ikirarin cewar shi ne Sarkin Kontagora, har zuwa lokacin da za a kammala shari’a,” cewar hukuncin da alkalin da ya zartar.
Lauyan masu shigar da kara, W. Y. Mamman, ya roki kotun da ta hana Barau gabatar da kansa a matsayin Sarkin Kontagora na bakwai.
Bayan zartar da hukuncin, alkalin ya dage shari’ar zuwa ranar 20 ga watan Oktoban 2021.