Kotu ta dakatar da Shugaban PPD a Nasarawa

Wata babban kotu ta biyu dake Lafia, fadar gwamnatin Jihar Nasarawa ta dakatar da Shugaban Jam’iyyar PDP na jihar, Mista Francis Orogu, inda ta kuma umurci a rufe sakatariyar jam’iyyar a jihar cikin gaggawa.  Alkalin dake sauraran kara a kotun, Mai Shari’a John biko ne ya bada umurnin, a lokacin da yake sauraran wata kara […]

Kotu ta dakatar da Shugaban PPD a Nasarawa

Wata babban kotu ta biyu dake Lafia, fadar gwamnatin Jihar Nasarawa ta dakatar da Shugaban Jam’iyyar PDP na jihar, Mista Francis Orogu, inda ta kuma umurci a rufe sakatariyar jam’iyyar a jihar cikin gaggawa. 

Alkalin dake sauraran kara a kotun, Mai Shari’a John biko ne ya bada umurnin, a lokacin da yake sauraran wata kara da tsohon dan takarar shugaban jam’iyya a jihar, Alhaji Sarki Mohammed ya shigar gabanta kwanakin baya, inda yake kalubalantar zabin Mista Francis Orogu a matsayin shugaban jam’iyyar a jihar. 

Har ila yau kotun ta hana Mista Orogu cigaba da bayyana kansa a matsayin shugaban jam’iyyar na jihar har sai bayan ta kammala sauraro da yanke hukunci akan karar. Sai dai a nasa bangaren, da wakilinmu ya tuntube shi don jin ta bakinsa game da batun shugaban jam’iyya na, Orogu ya bayyana cewa bai da masaniya game da wannan umurni daga kotun, inda ya kara da cewa babu wanda ya sanar ko ya ba shi takarda daga kotun dake tabbatar da wannan umurni. 

Daga nan sai ya yi amfani da wannan dama, inda ya bayyana cewa jam’iyyar a jihar ta dade da sallamar wanda ya shigar da karar wato Alhaji Sarki Mohammed daga kasancewa mambanta, tun ma kafin ya tsaya takarar shugabancin jam’iyyar, inda ya bukaci shugabanni da magoya bayan jam’iyyar a jihar da kasa baki daya, da su yi watsi da batun don a cewarsa babu gaskiya ciki, inda ya kara da cewa mahassada ne kawai wadanda ba sa son cigaban jam’iyyar a jihar da kasa baki daya ke kokarin bata ta a idon duniya.