Kotu ta dakatar da yada shirye-shiryen siyasa a gidan rediyo a Bauchi?
Kotun Majistare ta biyar da ke Jihar Bauchi, wadda Mai Shari’a Mohammed Mukhtar ke shugabanta, ta dakatar da shiryen-shiryen siyasa da dan Majalisar Tarayya mai wakliltar mazabar Misau da Dambam, Hon. Ahmed Yerima da kuma wanda Yahaya Magayakin Ajiya ke gabatarwa a gidan Rediyon Ray Power. Wadannan shirye-shirye da kotun ta dakatar da yada su […]

Kotun Majistare ta biyar da ke Jihar Bauchi, wadda Mai Shari’a Mohammed Mukhtar ke shugabanta, ta dakatar da shiryen-shiryen siyasa da dan Majalisar Tarayya mai wakliltar mazabar Misau da Dambam, Hon. Ahmed Yerima da kuma wanda Yahaya Magayakin Ajiya ke gabatarwa a gidan Rediyon Ray Power.
Wadannan shirye-shirye da kotun ta dakatar da yada su su ne ‘New APC Tambarin Yan kishin Jiha’, da kuma ‘Da mai kama ake kota’.
Dakatarwar ta biyo bayan wata kara ce mai lamba PDIBH/359/2017 da lauyan masu kara, Kwamared Aliyu Ilelah da Auwalu Jallah suka shigar da Yahaya Magayakin Ajiya da kuma Hon. Ahmed Yerima da kuma Gidan Rediyon na kamfanin Daar Communication, Ray Power FM Radio.
Lauyan masu kara Usman Bappah Darazo tun da farko ya roki kotun da ta dakatar da wadannan shirye-shirye har zuwa lokacin da aka kammala sauraron wannan kara, domin suna barazana ga zaman lafiya a jiha, bisa zargin cewa batutuwan da masu gabatar da shirin ke yadawa ya na tunzura jama’a da neman jama’a su yi watsi da APC a Jihar Bauchi da kuma yakar gwamnatin jiha.
Lauyan ya ce an bukaci wanda ake kara na daya da na biyu da su daina, amma suka ki, an kuma bukaci gidan rediyon ya daina ba su dama su na yada shirye-shiryen nan sun ki, an kuma kai koke-koke ga jami’an tsaro amma ba su dauki wani mataki akai ba, wanda ya janyo ana harzuka wadansu daga cikin ‘ya’yan Jamiyyar APC har su fara barazanar daukar doka a hannunsu, in ba ayi wani abu don dakatar da yada wadannan shirye-shiryen ba.
Lauyoyin wadanda ake kara, Barista Dauda Adamu da Barista Gambo Yaldami Yelmis sun nemi kotu ta yi watsi da karar, domin ba ta da hurumin da za ta saurari karar bisa doka, inda Lauya Dauda ya ce bisa la’akari da sashe na 13 na dokokin kotunan lardi na 189 na dokokin Jihar Bauchi na shekara ta 2006, abubuwan da masu kara ke so ayi musu baya cikin hurumin kotun, don kukan da suka kawo gaban kotun al’umma ya shafa bai shafi daidaikun mutane ba, kuma dukkan wadanda aka yi kara in banda gidan rediyon ‘ya’yan Jamiyyar APC ne, kuma jam’iyyar har yanzu ba ta warware rikicin cikin gida da ta ke fama da shi ba, kafin ta kai kara kotu. Kamar yadda yake a tsarin mulkin jamiyyar. Kuma wannan batun da suka yi kara akai ya shafi rikicin cikin jamiyya ne, wanda kotun ba ta da hurumi akai.
Shi kuwa Lauya Yelmis ya ce gidan rediyon bai taba bada dama ga wadanda ake kara na daya da na biyu su yada wani abu da zai kawo tashin hankali ko su kawo kiyayya ko batanci ga wani ko wata jami’yya ko yakar gwamnatin jiha ba, amma suna gudanar da ayyukansu ne kamar yadda doka ta tsara. Lauyan ya ce ba wani jami’in tsaro da ya musu magana kan shirye-shiryen nasu, kuma idan wadansu ‘ya’yan Jamiyyar APC suka dauki doka a hannunsu, to dama wadanda suka dauka ba ma su bin dokar ba ne, illa iya ka dai karya ce kawai suka yi.
To amma sai dai Alkalin Kotun, Mai Shari’a Muhammed Mukhtar ya bada umurnin dakatar da wadannan shirye-shiryen domin samun zaman lafiya, sannan ya daga sauraron karar har zuwa ranar 30 ga Watan Janairun 2018, domin ci gaba da sauraron karar. Koda yake wadansu daga cikin masana harkokin shari’a na ganin karar na iya samun koma baya sakamakon rasuwar daya daga cikin wadanda suka yi kara, Marigayi Alhaji Auwalu Jallah, Kakakin Jam’iyyar APC na Jihar Bauchi.