Kotu ta dakatar da yunƙurin hana zaɓen ƙananan hukumomin Kano
Babbar Kotun Jihar Kano ta hana duk wani yunƙurin hana hukumar zaɓen jihar gudanar zaɓen ƙananan hukumomi na ranar Asabar. Alƙalin kotun, Mai Shari’a Sanusi Ma’aji ne ya bayar da umarnin a ranar Juma’a, jajibirin zaben. Ya yanke hukuncin ne a kan ƙarar da hukumar ta shigar gabanta, inda take ƙalubalantar jam’iyyar APC da karin […]
Babbar Kotun Jihar Kano ta hana duk wani yunƙurin hana hukumar zaɓen jihar gudanar zaɓen ƙananan hukumomi na ranar Asabar.
Alƙalin kotun, Mai Shari’a Sanusi Ma’aji ne ya bayar da umarnin a ranar Juma’a, jajibirin zaben.
Ya yanke hukuncin ne a kan ƙarar da hukumar ta shigar gabanta, inda take ƙalubalantar jam’iyyar APC da karin mutane 13, da ke neman a hana gudanar da zaɓen.
Kazalika, alƙalin ya bai wa jami’an tsaron umarnin gaggauta bai wa rayuka da dukiyoyin al’umma tsaron da ya kamata a zaben da ke tafe.