Kotu Ta Daure Barawon Awaki A Gidan Kaso

Ya haura gidan makwabta ya sace awaki biyu

Kotu Ta Daure Barawon Awaki A Gidan Kaso

Kotu ta daure wani matashi mai shekara 20 a gidan yari saboda satar awakin makwabta a garin Jos, Jihar Filato.

Majistare da ke zamanta a Jos ta tisa keyar matashin zuwa gidan kawo na tsawon wata tara, bayan samun sa da laifin da ake tuhumar sa.

Guda daga cikin alkalan kotun, Adam Sadiq ne ya yanke hukuncin, tare da ba wa matashin zabin biyan tarar N10,000 gami da biyan mai awakin diyyar N40,000.

Tun da fari dai dan sanda mai gabatar da kara, Insfekta Ibrahim Gokwat, ya bayyana wa kotun cewa wani mai suna Dung Gyang ne ya kai korafin ofishinsu da ke Anglo-Jos ranar 11 ga watan Oktoba.

Ya kara da cewa binciken su ya tabbatar wanda ake tuhumar ya haura gidan mai karar, ya sace masa awaki biyu da suka kai darajar N40,000, laifin da ya ce ya saba wa sashe na 334 da kuma 271 na kundin Penal Code.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos