Kotu ta daure barayin batirin mota shekara 1
Wata kotu a garin Jos, Jihar Filato, ta daure wasu abokai biyu kan satar batirin mota da cajarsa na kimanin N85,000 da ake zargin su. Alkalin kotun ya daure matasan ne bayan sun amsa zargin da kuma na hadin baki, sata, shiga wuri ba tare da izini ba. Mataimakin Gwamnan Sakkwato ya bar PDP Mutum […]
Wata kotu a garin Jos, Jihar Filato, ta daure wasu abokai biyu kan satar batirin mota da cajarsa na kimanin N85,000 da ake zargin su.
Alkalin kotun ya daure matasan ne bayan sun amsa zargin da kuma na hadin baki, sata, shiga wuri ba tare da izini ba.
Sai dai Alkalin ya ba su zabin biyan tarar N20,000 kowannensu ko daurin watanni uku kan laifin hadin baki, sai kuma zabin biyan N10,000 ko daurin watanni shida kan laifin shiga wuri ba tare da izini ba.
Dan Sanda mai gabatar da kara Insfekta Labaran Ahmad ya bayyana wa kotu cewa matasan sun aikata laifin ne bayan wani mutum ya ajiye motarsa a gefen wani masallaci da ke Anguwan Rogo don yin sallah.
Laifin da ya ce ya saba wa dokokin kundin Penal Code.