Kotu ta daure dan damfara shekara 235 a kurkuku

Ana zarfinsa ne da aikata damfarar miliyan 525

Kotu ta daure dan damfara shekara 235 a kurkuku

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Uyo, babban birnin Jihar Akwa Ibom, ta yanke wa wani mutum da ta samu da laifin damfarar kasa da kasa hukuncin daurin shekara 235 a gidan kaso.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Agatha Okeke ce ta yanke hukuncin yayin zaman kotun na ranar Laraba.

Kotun dai ta sami mutumin ne mai suna Scales Olatunji da laifin damfarar kudaden da yawansu ya kai Naira miliyan 525.

An gurfanar da Scales Olatunji ne ranar biyu ga watan Yulin 2019 ana tuhumarsa da laifuka 45 masu alaka da aikata sojan gona, hada baki da kuma zambar kudade.

Sai dai ya musanta aikata laifukan da aka zarge shi da aikatawa.

Sarakunan Nijar sun kai wa Gwamnatin Yobe ziyarar jaje

Ɗan majalisa ya yi jinjina kan naɗa Danyaya Sarkin Ningi

’Yan Sanda sun kama gungun ’yan fashi 7 a Katsina

Zaɓen Edo: Ana ci gaba da ƙirga ƙuri’u