Kotu ta daure DJn da ya hana Islamiyya sakat da kida a Kano

Kotu ta daure DJn da ya hana Islamiyya sakat da kida

Kotu ta daure DJn da ya hana Islamiyya sakat da kida a Kano

DJ

Wata Kotun Shari’ar Musulinci da ke unguwar Danbare a Kano ta aike da wani mai kidan DJ zuwa gidan kaso, saboda sakin kida da yake yi yana damun daliban wata Islamiyya.

Kotun, wacce ke karkashin jagorancin Mai Shari’a, Mallam Munzali Idris Gwadabe, ce ta yanke hukuncin a ranar Laraba.

Mai gabatar da kara, Insifekta Bashir Wada bayan ya karanto wa wanda ake zargin kunshin tuhumar da ake yi masa, bai wahalar da kotu ba ya amsa.

Ana zargin sa da hana masu karatu kunna amsa-kuwwa a lokacin da yake gudanar da kidan DJ inda ya ce wai suna takura masa har ya kara da cewa, wai karfin amsa-kuwwar masu karatun yana danne nasa.

Wannan dalilin ne yasa aka gurfanar da shi a gaban a gaban kotun.

Mai Shari’a Munzali Gwadabe ya aike da shi zuwa gidan gyaran hali har zuwa ranar 6 ga watan Yuli, 2023 domin ya yanke masa hukunci.

Tags