Kotu ta daure Fasto shekara biyu saboda satar babur

Kotun Lardi ta Gargajiya (Upper Customary Court), da ke G.R.A, Zariya, ta daure wani Fasto mai suna Fasto Michael Yohanna tsawon shekara biyu da rabi saboda samunsa da satar babur.dan sanda mai gabatar da kara a kotun Saje Bashir Abdullahi ne ya gabatar Fasto Michael Yohanna bisa tuhumarsa da haurawa gidan makwabcinsa inda ya sace […]

Kotu ta daure Fasto shekara biyu saboda satar babur
Kotu ta daure Fasto shekara biyu saboda satar babur

Kotun Lardi ta Gargajiya (Upper Customary Court), da ke G.R.A, Zariya, ta daure wani Fasto mai suna Fasto Michael Yohanna tsawon shekara biyu da rabi saboda samunsa da satar babur.
dan sanda mai gabatar da kara a kotun Saje Bashir Abdullahi ne ya gabatar Fasto Michael Yohanna bisa tuhumarsa da haurawa gidan makwabcinsa inda ya sace masa babur.
Saje Bashir Abdullahi, ya ce a ranar 20 ga Fabrairun bana da misalin karfe 12:00 na rana wani mai suna Auwal Shehu wanda yake zaune a Unguwar Barde da ke garin Fambeguwa a karamar Hukumar Kubau a Jihar Kaduna, ya zo babban ofishin ’yan sanda da ke shiyya ta daya da ke Zariya yana kukan da cewa a ranar 11/2/2016 da misalin karfe 7:00 na dare ya aje babur dinsa kirar Boksa mai launin ja da kudinsa ya kai Naira dubu 60  a gidansa da ke Unguwar Barde a Fambeguwa, amma da gari ya waye da misalign karfe 5:00 na asuba a ranar 12/2/2016 sai ya ga an hauro katangar gidansa an sace masa babur. Y ace yana cikin nema har zuwa ranar 29/2/2016 inda ya kama babur din a hannun makwabcinsa mai suna Fasto Michael Yohanna lokacin da yake kan babur din.
Ya ce a lokacin da aka zo ofishin ’yan sanda ne sai Fasto Michael Yohanna ya amince cewar lallai shi ne ya haura gidan ya sace babur din. dan sandan ya ce wannan laifi ne da ya saba wa sashi na 287.
Wanda ake tuhuma Fasto Michael Yohanna ya amsa laifinsa, a gaban kotun ba tare da bata lokaci ba, inda a zaman kotun na farko alkalin kotun Mai shari’a Atiku Sarki Yohanna ya dage shari’ar zuwa ranar 7/3/2016, kuma bayan an dawo a ranar ce alkalin kotun bayan ya same shi da laifin haura wa gida da satar babur ya hukunta shi da daurin shekara biyu da rabi ko zabin biyan tara ta Naira dubu 30.