An daure jami’an EFCC na bogi shekaru 30

An kama su a  lokacin da suka je aiwatar da umarnin kotun bogi

An daure jami’an EFCC na bogi shekaru 30

daurin rai da rai

Kotu ta yanke hukuncin daurin shekaru 30 ga wasu mutane biyu da aka kama suna yin sojan gona a matsayin jami’an hukumar yaki da masu karya tattalin arziki (EFCC).

Dubun jami’an EFCC na bogi — Ugwu Chijioke da Ibrahim Adekunle — ta cika ne a  lokacin da suka je domin zartar da wani jabun umarnin kotu a unguwar Lekki da ke Legas a watan Mayun 2021.

Abubuwan da aka kama a hnnun wadannan jami’an EFCC na bogi sun hada da jabun katin shaidar aiki da rigunan hukumar da kuma takardar umarnin gobi daga Kotun Majistare da ke zamanta a Mushin.

Hukumar ta gurfanar da su a gaban Kotun Laifuka na Musamman da ke Ikeja, kan laifuka biyar na yin damfara, sojan gona, mallakar takardun bogi amfani da kayan EFCC ba bisa ka’ida ba.

Bayan sun amsa duk laifukan, Mai Shari’a O.O. Abike-Fadipe ya yanke musu hukundin daurin jimillar shekaru 46 kowannensu.

Alkalin ya yanke musu hukucin daurin shekara takwas kan laifi na biyar, shekaru bakwai-bakwai a kan laifuka na 1 zuwa na 3, da kuma shekara guda kan laifi na hudu.

Sai dai alkalin ya bayyana cewa kirgen shekarun zaman gidan yarin da za su yi zai gudana ne a tare lokaci guda, ba a jere ba.