An daure Janar din soja kan satar N1.7bn
An yanke wa Manjo-Janar Umar Muhammad hukuncin daurin shekara bakwai kan satar dukiyar kamfanin kula da kadarorin Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya
Kotun Sojin Najeriya ta yanke hukuncin daurin shekaru bakwai ga Manjo-Janar Umar Muhammad, tsohon Manajan Daraktan Kamfanin Kula da Kadarorina (NAPL), kan satar dukiyar kamfanin.
Kotun da kuma umarce Manjo-Janar Umar Muhammad, wanda ya gurfana a gabanta a kan keken guragu, da ya mayar da Naira biliyan 1.7 (Dala miliyan 2.2) zuwa asusun Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya.
Rundunar ta gurfanar da Manjo-Janar Umar Muhammad ne kan zargin sa da laifuka 18 da suka ha da amfani da takardun bogi, karkatar da kudade da kuma hada baki domin aikata laifi, zargin da ya musanta da farko.
Amma a zaman kotun sojin na ranar Talata, kwamitin alkalai takwas karkashin jagorancin Manjo-Janar James Myam sun kama shi da 14 daga cikin laifuka 18 da aka gurfanar da shi a kansu.
Bayan sauraron shaidu 24 daga bangaren masu kara da kuma shaida biyu na wanda ake gurfanarwa, Janar Myam ya ce laifukan da Manjo-Janar Umar Muhammad ya aikata sun saba kundin tsarin mulkin Najeriya da kuma dokar aikin soji.
Daga nan ya yanke hukuncin daurin shekara bakwai, kan kowanne daga wasu cikin laifukan, wasu shekara biar wasu kuma shekaru biyu.
Janar Myam ya ce hukuncin zai tabbata ne bisa sahalewar mahukunta.
Kafin yanke hukuncin na yanzu dai, Janar Muhammad ya shafe shekaru biyu a tsare a Barikin Sojoji na Mogadishu da ke Abuja.