Kotu Ta Daure Lebura Kan Satar Wake Kwano 7

Wata kotun majistare ta yanke wa wani matashin lebura hukuncin daurin wata hudu, kan satar kwano bakwai na wake.

Kotu Ta Daure Lebura Kan Satar Wake Kwano 7

KOTU

Wata kotu ta yanke wa wani matashin lebura hukuncin daurin wata hudu a gidan yari kan satar kwano bakwai na wake.

Dan sanda mai gabatar da kara ya shaida wa kotun cewa dubun matashin mai shekara 20 ta cika ne ne bayan ya balle shagon mai kara ya sace masa kwano bakwai na Wake da manja da kiret-kiret na lemo da sauran kayan abinci.

Ya kara shaida wa kotun da ke zamanta a Jos, Jihar Filato, cewa sun gano baya ga kayan abincin, wanda ake zargin ya saci tukunyar gas da talabiji na bango da kudinsu ya kai N172,000.

Laifin,a  cewarsa ya saba wa sashi na 333, da na 336, da na 273 na kundin Penal Code.

Bayan sauraron karar, kotun ta yanke wa leburan hukunci, tare da ba shi zabin biyan tarar N30,000, da kuma karin wata N30,000 din ga wanda ya yi wa satar, ko ta kara masa wata guda kan daurin.

Alkalin ya ce ya yanke hukuncin ne domin ya zamo izina ga masu aikata laifuka irin haka.