Kotu ta daure leburori na wata 7 kan satar akuya a Jos
Wata kotu a Jos, Jihar Filato, ta daure wasu leburori biyu na tsawon wata bakwai a kurkuku bisa laifin satar akuya. Yayin zaman kotun a ranar Talata, Manji Manshak dan shekara 21 da Zimshak Zingak mai shekara 23, duk zan amsa laifin da aka tuhume su da aikatawa. ISWAP ta kashe Matafiya biyu a Borno […]
Wata kotu a Jos, Jihar Filato, ta daure wasu leburori biyu na tsawon wata bakwai a kurkuku bisa laifin satar akuya.
Yayin zaman kotun a ranar Talata, Manji Manshak dan shekara 21 da Zimshak Zingak mai shekara 23, duk zan amsa laifin da aka tuhume su da aikatawa.
Kotun karkashin jagorancin masu shari’a Malam Ghazali Adam da Mista Hyacinth Dolnaan, sun yanke wa masu laifin biyan tarar N20,000.
Tun farko, dan sanda mai gabatar da kara Insfekta Monday Dabit, ya fada wa kotun cewa a ranar 23 ga Afrilu wani mai suna Mista Alex Emmanuel ya kai kara ofishin ’yan sanda da ke Anglo, Jos, cewa an sace wata akuya an kuma yanka ta.
Ya ce, wannan laifi ne mai hukunci a karkashin Sashe na 59 da na 272 na ‘Penal Code’ na Jihar Filato.