Kotu ta daure magidanci da matarsa kan sayar da gidansu ga mutum uku

Babbar kotun lardi na birnin tarayya da ke garin Gwagwa Abuja ta yanke wa wani magidanci da matarsa hukuncin daurin wata tara, bayan ta same su da laifin sayar da gida guda ga mutum uku. Jami’ar shigar da kara daga ma’aikatar shari’a ta tarayya Misis Dabid Kafanchan wanda ta gurfanar da mutane biyun a ranar […]

Kotu ta daure magidanci da matarsa kan sayar da gidansu ga mutum uku
Kotu ta daure magidanci da matarsa kan sayar da gidansu ga mutum uku

Babbar kotun lardi na birnin tarayya da ke garin Gwagwa Abuja ta yanke wa wani magidanci da matarsa hukuncin daurin wata tara, bayan ta same su da laifin sayar da gida guda ga mutum uku. Jami’ar shigar da kara daga ma’aikatar shari’a ta tarayya Misis Dabid Kafanchan wanda ta gurfanar da mutane biyun a ranar Larabar makon jiya, ta sanar da kotun cewa wanda ake zargi na farko mai suna Emeka Nnadi ya karbi adadin kudi Naira dubu 850 a rarrabe daga hannun mutum uku a matsayin kudin gidan, a yayin da wadda ake zargi ta biyu kuma wadda matarsa ce, mai suna Tochi Nnadi ta kasance shaida kuma wadda ta rubuta rasitan ciniki guda ukun, kamar yadda takardun shaidan biyan kudin ya nuna wanda masu kara suka gabatar a babban ofishin ’yan sanda, inji ta.
Mai shigar da karar ta ce aikata hakan laifuffuka ne da suka saba da kundin tsarin mulki na Penal Code a sashi na 79 da 312 da kuma 312. Haka nan kotun ta samu bayanin cewa  dukkanin mutane uku ba su iya zama a gidan ba bayan sun biya kudin ga wadanda ake zargin, kasancewar mutum na hudu da ya sayi gidan yana zaune a ciki, a yayin da mutum na biyar kuma ya samu nasarar amsar kudin da ya bayar Naira dubu 200, bayan ya samu labarin cewa wanda ake tuhuman na shirin barin garin tare da iyalansa zuwa birnin Cotonue da ke kasar Benin.
Da Alkalin Kotun mai shari’a Muhammad Sulaiman Ola ya waiwaye su, wadanda ake kara sun amince da aikata laifin, sai dai sun nemi kotun da ta yi musu sassauci. Mai shari’a ya ba da umarnin su biya Naira dubu 10 a kan kowane laifi daga cikin laifuffuka uku da aka same su da aikatawa, ko kuma su yi zaman gidan wakafi  na wata shida. Haka nan mai shar’a ya kuma tilasta masu su biya mutane uku da ke kara Naira dubu 200, da Naira dubu 350, Sai kuma Naira dubu 300 a matsayin kudi da suka karba daga wajen masu karan, kamar yadda suka amince sun karba a yayin shari’ar, cikin kwana sha biyu masu zuwa ko kuma su yi zaman wakafi na wadansu watanni uku. Mai shari’a ya ce hukuncin dauri na laifin farfo zai gudana a lokaci guda da hukuncin dauri na biyu.