Kotu ta daure magoya bayan ’Yan’uwa Musulmi 68
Wata kotu a kasar Masar ta yanke wa wasu magoya bayan ’yan kungiyar ’Yan’uwa Musulmi su 68 hukuncin zama a gidan kaso, bayan da ta same su da laifin ta da zaune tsaye a bara, bayan hanbarar da Shugaba Muhammad Mursi.Duka mutanen an same su da laifin a kisan mutum 30 da kuma aniyyar kashe […]
Wata kotu a kasar Masar ta yanke wa wasu magoya bayan ’yan kungiyar ’Yan’uwa Musulmi su 68 hukuncin zama a gidan kaso, bayan da ta same su da laifin ta da zaune tsaye a bara, bayan hanbarar da Shugaba Muhammad Mursi.
Duka mutanen an same su da laifin a kisan mutum 30 da kuma aniyyar kashe wasu mutane a birnin Alkahira, ranar 6 ga watan Oktoban bara, a lokacin da fiye da mutum 50 suka rasa rayukansu a fadin kasar a wata arangama tsakanin magoya bayan Shugaba Mursi da masu adawa da shi.
Alkalin Kotun Mohammed Ali al-Faki ya bai wa mutum 63 daga cikinsu daurin shekara 15 sauran biyar kuma daurin shekara 10. Kodayake kasashen duniya da dama da kuma kungiyoyin Kare Hakkin dan Adam suna bayyana damuwarsu kan murkushe ’yan adawa da Gwamnatin Abdel Fattah el-Sisi take yi tun bayan darewarta karagar mulki a watan Yulin bara.
A halin yanzu dai, akwai dimbin magoya bayan ’yan kungiyar ’Yan’uwa Musulmi da ke tsare a gidan yarin kasar Masar.