Kotu ta daure malamin da ya yi lalata da dalibarsa

Babbar Kotun Majistare ta Dutse ta daure wani malamin karamar sakandaren ’yan mata ta danzomo da ke karamar Hukumar Sule Tankarkar saboda samunsa da laifin yin lalata da dalibarsa mai shekara 12 a ban-dakin ofishinsa da ke makarantar.  Malamin mai suma Aminu Lawal ana zargin cewa ya saba aikata irin wannan danyen aiki inda aka […]

Kotu ta daure malamin da ya yi lalata da dalibarsa
Kotu ta daure malamin da ya yi lalata da dalibarsa

Babbar Kotun Majistare ta Dutse ta daure wani malamin karamar sakandaren ’yan mata ta danzomo da ke karamar Hukumar Sule Tankarkar saboda samunsa da laifin yin lalata da dalibarsa mai shekara 12 a ban-dakin ofishinsa da ke makarantar. 

Malamin mai suma Aminu Lawal ana zargin cewa ya saba aikata irin wannan danyen aiki inda aka jima ana tarkonsa sai a wannan karo dubunsa ta cika, inda jami’an tsaron makarantar suka kama shi suka mika wa hukumar makarantar.
Hukumar NSDSC ce ta gurfanar da malamin a gaban kotun tare da gabatar da yarinyar wadda aka sakaye sunanta a matsayin shaida inda malamin mai shekara 35 ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi.
Alkalin kotun Mai shari’a Amina dahiru ta ce laifin da malamin ya aikata ya saba wa sashi na 285 na kundin manyan laifuffuka saboda haka kotun ta daure shi shekara biyu, ba tare da zabin biyan tara ba.
A wata sabuwa jami’an tsaron na NSDSC sun kama wani dan Kano zuwa Jiddah da ake zargin ya kware wajen damfarar mata yana amsar kudin kujera da sunan zai kai su Makka.
Mutumin mai suna Suleiman Yahaya dan asalin karamar Hukumar Zango da ke Jihar Katsina an kama shi ne a lokacin da ya damfari wata mace mai suna Hajara Ibrahim mai shekara 59 a karamar Hukumar Roni da ke Jihar Jigawa Naira dubu 750, da sunan zai kai ta Makka amma tsawon shekaru uku bai kai ta ba, sai da ta hada shi da jami’an tsaro suka kama shi.
Sai dai wanda ake zargin mai kimanin shekara 55 ya ce Naira dubu 320 ya amsa a wajen Hajara a matsayin kudin ajiya, kuma saboda lokacin tafiyarsa zuwa Saudiyya ya yi ne ya tafi bai dawo ba sai bayan shekara biyu shi ne da ya dawo aka kama shi amma ya dawo wa matar da Naira dubu 100, kuma ya bukaci a ba shi lokaci zai dawo mata da ragowa kudinta nan bada dadewa ba.