Kotu ta daure masu safarar miyagun kwayoyi shekara 141
Kotunan dai sun same su da laifukan safara, mallaka da kuma hada-hadar miyagun kwayoyi.
Manyan Kotunan Tarayya da ke zamansu a biranen Benin na Jihar Edo da Abeokuta a Jihar Ogun, sun daure wasu mutum biyar da aka samu da laifin safarar miyagun kwayoyi shekara 141.
Kotunan dai sun sami wata budurwa mai shekara 25, Chioma Okocha, da Ndubuisi John da Haruna Aliyu da Saddam Abdullahi da kuma Bashir Usman da laifin safarar Hodar Iblis da Tabar Wiwi.
- An kai harim bom kusa da Majalisar Dokokin Uganda
- Mutane da dama sun mutu bayan fashewar tankin iskar gas a Legas
An dai yanke wa Chioma hukuncin shekara 15 ne.
Babbar Kotun Benin ce dai ta daure ta shekara 15 bayan jami’an hukumar NDLEA sun kama ta da giram 200 na Hodar Iblis a watan Satumban 2021.
Kakakin hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi a ranar Talata a Abuja ya ce wacce ake zargin ta amsa laifin da ake zarginta da shi ranar Litinin, 15 ga watan Nuwamba.
“Amma alkalin ya ba ta zabin biyan tarar Naira miliyan biyu ko shafe shekara 15.
“Su kuma ragowar mutum biyun, Babbar Kotun Tarayya da ke Abeokuta, karkashin Mai Shari’a Ogunremi Omowunmi Oguntoyinbo ta same su da laifi tare da daure su shekara 126.
“An kama su ne a kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan sun kokarin yin safarar kulli 46 na Tabar Wiwi mai nauyin kilogiram 552, inda aka zarge su laifuka uku na safara, mallaka da kuma hada-hadar miyagun kwayoyi,” inji Babafemi.
Ya ce alkalin ta yanke wa wanda ake zargin na daya da na biyu da na uku hukuncin shekara 30 kowannensu, yayin da direban motar aka daure shi shekara 21, yaron motar kuma shekara 15.