Kotu ta daure masu unguwanni uku kan rikicin fili a Kaduna

Alkalin Kotun Titin Daura a garin Kaduna Mai shari’a Murtala J. Zubairu ya yanke hukuncin daurin shekara daidai ga Sarkin Mahuta, Mahmuda Sama’ila da masu unguwanni biyu, Wada Masaba da Inuwa Haladu dukkansu mazauna garin Mahuta a Jihar Kaduna da wadansu mutum 13 bisa samunsu da laifin hadin baki da kokarin cin zarafi da shiga […]

Kotu ta daure masu unguwanni uku kan rikicin fili a Kaduna
Kotu ta daure masu unguwanni uku kan rikicin fili a Kaduna

Alkalin Kotun Titin Daura a garin Kaduna Mai shari’a Murtala J. Zubairu ya yanke hukuncin daurin shekara daidai ga Sarkin Mahuta, Mahmuda Sama’ila da masu unguwanni biyu, Wada Masaba da Inuwa Haladu dukkansu mazauna garin Mahuta a Jihar Kaduna da wadansu mutum 13 bisa samunsu da laifin hadin baki da kokarin cin zarafi da shiga filin da ba nasu ba.
Wadanda ake zargin da wadansu mutum shida sun kwashe shekara biyu suna shari’a a kan rikicin wasu fulotai 120 da aka yanka a garin na Mahuta.
Mai sharia Murtala J. Zubairu a hukuncinsa a takarda Mai Lamba KMD/30359/2014 , ya ce duk da cewa wadanda ake zargin sun musanta laifin da ake yi musu, amma ya same su da laifin cin amana da hadin baki domin yin rashin gaskiya wadanda suka saba wa sashi na  96 da na  97 na dokokin Final Kod.
Ya ce laifin shiga filin da ba nasu ba ya saba wa sashi na  342 wanda hukuncinsa yake sashi na 348 na Final Kod, sannan laifin aikata ba daidai ba da cin zarafi wanda ya saba wa sashi na 396, hukuncinsa ke sashi na  397 na Final Kod.
“Kafin in yanke hukunci a kan wadanda ake zargi zan so da farko inji ko wadanda ake zargi suna da abin cewa sannan ko an taba samunsu da laifi a baya irin wannan,” inji shi.
Mai Sharia ya yi bayanin hukuncin a kan hada baki domin yin cuta da cewa wata shida ne a gidan yari tare ko tara ko kuma a hada duka.
Ya ce hukuncin shiga filin da ba bisa yarda ba, hukuncinsa ba ya wuce shekara daya a gidan yari ko tara ko kuma duka, sai hukuncin cin zarafi ko nuna isa, zai iya wuce shekara biyu ko tara ko kuma duka.
Mai Shari’ar ya tambayi lauyan masu kara Barista Mohammed Tajuddeen ko wadanda ake kara sun taba aikata irin wannan laifi a baya, sai ya ce bai sani ba.
Shi kuwa lauyan wadanda ake kara Barista Egustina Joshua ya shaida wa kotu cewa wadanda ake kara mutane ne da ke da mutunci cikin jama’a kuma suna da iyalai sannan karon farko ke nan da suka aikata irin wannan laifi don haka sai ya nemi kotu ta yi musu sassauci.
Daga nan sai Alkalin ya yanke musu hukuncin daurin wata hurhudu a gidan yari a kan laifin hada baki domin yin cuta ko su biya tarar Naira dubu biyar-biyar kowannensu.
Ya ce laifin shiga muhallin da ba nasu ba kuwa ya daure su wata takwas-takwas ko tarar Naira dubu 15 kowannensu, yayin da laifin cin zarafi ya yanke musu hukuncin wata 12 a gidan maza ko tarar Naira dubu 30 ga kowannensu. Sai dai dukkan wadanda ake zargin sun biya tarar da aka yanke musu domin kauce wa zuwa gidan yari.

An kama masu garkuwa da mutane a Borno 

Rikicin ya kunno kai a Hukumar Alhazan Jihar Delta

Sojoji sun ceto mutane 5 da ISWAP ta sace a Harin Ngoshe

Iran da Amurka sun daidaita tattaunawar sulhu a Switzerland