Kotu ta daure mata kan yin alfasha da jariri

Wata kotun Majistare da ke zamanta a Dutse babban birnin Jihar Jigawa ta tsare wata mata a kurkuku bisa zargin nuna rashin imani ga wani jariri mai kwan 10 da haihuwa. Ana tuhumar matar da ke zaune a unguwar Jama’are ta Karamar Hukumar Hadeja  da tilasta wa jaririn tsotsar gabanta. An ceto jaririn da aka […]

Kotu ta daure mata kan yin alfasha da jariri

Jariri

Wata kotun Majistare da ke zamanta a Dutse babban birnin Jihar Jigawa ta tsare wata mata a kurkuku bisa zargin nuna rashin imani ga wani jariri mai kwan 10 da haihuwa.

Ana tuhumar matar da ke zaune a unguwar Jama’are ta Karamar Hukumar Hadeja  da tilasta wa jaririn tsotsar gabanta.

Dan sanda mai shigar da kara, Kabiru Warwade ya shaida wa kotun cewa mahaifiyar jaririn ce ta kama wadda aka zargin tana tsaka da aikata danyen aikin.

Ya kuma ce wadda ake zargin ta aikata laifin ne da misalin karfe 10:30 na safiyar ranar Talata, takwas ga watan Satumba, 2020.

A cewarsa, “rashin imani da halin ko-in-kula” da matar ta yi wa jarirn sun saba wa Sashe na 285 da kuma 238 na Kundin Dokokin Penal Code.

To sai dai matar da ake zargin ta musanta aikata laifin.

Daga nan ne alkalin kotun, Mai Shari’a Akilu Isma’il ya dage sauraron karar har zuwa ranar biyar ga watan Oktoba domin ci gaba da sauraron shari’ar.

Ya kuma ba da umarnin a tisa keyar wacce ake zargin zuwa kurkuku.

An yi garkuwa da ’yar ƙasar waje a Nijar

Sojin sama sun yi kuskuren kashe mutum 16 a Zamfara

Rikicin Masarautar Kano: Tsagin Aminu Ado Bayero zai ɗaukaka ƙara

Yadda Jimmy Carter ya ceto rayuwata – Obasanjo