Kotu ta daure matar aure shekara 3 saboda satar jariri

Kotun Majastare ta Ado-Ekiti a Jihar Ekiti, ta yanke hukuncin daurin shekara uku ga wata matar aure mai suna Mercy Momoh da aka same ta da laifin satar jariri dan wata daya ta hanyar yaudara. Matar mai shekara 39 ta amsa laifinta a lokacin da aka gabatar da ita gaban kotun a ranar Litinin da […]

Kotu ta daure matar aure shekara 3 saboda satar jariri

Kotun Majastare ta Ado-Ekiti a Jihar Ekiti, ta yanke hukuncin daurin shekara uku ga wata matar aure mai suna Mercy Momoh da aka same ta da laifin satar jariri dan wata daya ta hanyar yaudara.

Matar mai shekara 39 ta amsa laifinta a lokacin da aka gabatar da ita gaban kotun a ranar Litinin da ta gabata.

Tun farko sai da dan sanda mai gabatar da kara Samson Osobu, ya shaida wa kotun cewa, Mercy Momoh ta aikata laifin da ake zarginta ne a ranar 20 ga Satumban da ya gabata a Sakatariyar Gwamnatin Jihar da ke Ado-Ekiti. Ya shaida wa kotun cewa, Mercy ta hadu da Funmilayo Dada, mahaifiyar jaririn a kan hanya ce inda ta gayyace ta zuwa samun tallafin kudi da gwamnati ke bayarwa.

A nan take ta amince suka jera zuwa ofishin da ake gudanar da shiri a Sakatariyar Gwamnati inda matar ta aiki mahaifiyar jaririn ta sayo mata katin waya ta ce ta bar jaririn tare da ita.

Bayan dawowa daga aikar ce ta nemi mata da danta sama da kasa ba ta gansu ba wanda ya sa ta kai rahoton lamarin ga ’yan sanda.

Bayan binciken ne ’yan sanda suka gano matar goye da jaririn a hanyarta ta tserewa, inda suka ceto jaririn suka mika shi ga mahaifiyarsa Funmilayo Dada. Da yake yanke hukunci, Alkalin Kotun Mai shari’a Adesoji Adegboye ya daure Mercy Momoh  shekara 3 a gidan yari tare da zabin biyan tarar Naira dubu 100.