Kotu ta daure matashi kan satar abinci

Bayan ya sace abincin gidan ya Banks wa gidan wuta

Kotu ta daure matashi kan satar abinci

Kurkuku

An gurfanar da wani matashi a kotu kan sace kayan abinci a wani gida da kuma kone gidan a Jihar Kwara.

Hukumar tsaro ta Sibil Difens ta gurfanar da matashin ne kan sata da kayan gidan, inda alkali ya tusa ƙayarsa zuwa Gidan Yarin Mandala da ke jihar.

Mai Shari’a na kotun Majistaren ya yanke hukuncin daurin shekara guda ba tare da zaɓin biyan tara  ne bayan da ya samu matashin da laifi.

A ranar 26vga watan Satumba 2024 ne matashin ya fasa gidan a cikin dare a yankin Onireke, Upper Gaa Akanbi, da ke Karamar Hukumar Ilorin ta Kudu.

Ya saace kayan abinci da kayan daƙi da sauransu, sannan ya Banks wa gidan wuta.

Ya banka wa gidan wuta ne a kokarinsa na tserewa bayan  jama’a sun yi yunkurin kama shi.

Amma daga bisani an yi nasarar kama shi aka damƙa wa jami’an Sibil Difens.

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano

Gwamnatin Kano na shirin tara harajin 80bn a 2025

Kirsimeti: Zulum ya ɗauki nauyin jigilar fasinjoji 710 zuwa garuruwansu

Ɗan shekara 60 ya rasu a hatsarin kwalekwale a Sakkwato