Kotu ta daure matashi wata 6 kan satar magi da sabulu
An yanke masa hukuncin saboda satar kwalin magi da na sabulun wanka.
Wata kotu da ke zamanta a garin Jos a Jihar Filato ta yanke wa wani matashi mai shekara 22 hukuncin daurin wata shida a gidan yari bisa laifin satar kwalin magi da kuma kwalin sabulun Dudu-Osun da kudinsu ya kai N55,000.
Alkalin kotun, Shawomi Bokkos, ta yanke wa matashin hukuncin ne bayan ya amsa laifinsa tare da rokon kotun da ta yi masa sassauci.
- DAGA LARABA: Da Gaske Shan Garin Kwaki Na Kashe Ido?
- Dahiru Bauchi ya nemi Tinubu ya biya jinin Musulmin da jirgin soji ya kashe a Kaduna
Ta kuma bai wa mai laifin zabin biyan tarar N20,000.
Tun da farko, dan sanda mai shigar da kara, Ibrahim Gokwat, ya shaida wa kotun cewa wani Mista Gbenga Ayantola ne ya kai kara ofishin ’yan sanda na “A” a ranar 10 ga watan Oktoba.
Ya ce wanda ake tuhumar ya kutsa cikin shagonsa inda ya saci katon na magi da kuma sabulun wanka wadanda kudinsu ya kai N55,000.
Dan sandan ya shaida wa kotun cewa a lokacin da ’yan sanda ke gudanar da bincike, wanda ake zargin ya amsa laifinsa.
Ya ce laifin ya ci karo da dokar ‘Penal Code’ na laifuka.