Kotu ta daure ‘barawon’ kaji a gidan yari
Kotun ta kama matashin da laifin satar kaji a wani caji ofis a Abuja.
Kotu ta yanke wa wani matashi daurin wata daya saboda samun shi da laifin satar kaji a ofishin ’yan sanda.
Da yake yanke hukuncin, alkalin kotun da ke zamanta a yankin Bwari, Abuja, Alkalin kotu, Hassan Aliyu, ya ce hukuncin zai zama izina ga masu halin bera irin na matashin.
- Dalilin da ya sa ake tsoron aurenmu —Mata ’Yan Boko
- Kotu ta raba auren shekaru 12 saboda saurin fushin mata
- Ya gurfanar da matarsa a gaban kotu bisa zargin yunkurin kashe shi
- Tsaftar Muhalli: Kotu ta rufe tashar mota da gidan mai a Kano
Bayan gabatar da tuhumar da ake zargin sa da aikatawa, matashin bai bata lokaci wajen amsa cewar ya aikata laifin ba.
Lauya mai shigar da kara, Tunde Arowolo, ya bayyana cewa an shigar da kara a kan matashin kan satar kajin a caji ofis din ‘yan sanda da ke Bwari.
Sai dai wanda ake tuhumar, ya ce ya tsinci kajin ne a kan titi.
Alkalin kotun ya ce laifin ya saba da sashe na 287 na kundin laifuka, don haka ya yanke wa matashin hukuncin zuwa gidan kaso na wata daya ko biyan tarar N5,000.