Kotu ta daure mutane 4 a Masar saboda aikata dabi’un ‘yan luwadi

Wata kotu a kasar Masar ta yanke wa wasu mutane hudu hukuncin shekaru takwas a gidan kaso sakamakon samunsu da ta yi da laifin aikata wasu dabi’u da suke kama da na ‘yan luwadi.An samu mutanen ne da laifin halarta wani bikin farti inda sukai wata shiga cikin tufafin mata, sai kuma laifin caba kwalliya […]

Kotu ta daure mutane 4 a Masar saboda aikata dabi’un ‘yan luwadi
Kotu ta daure mutane 4 a Masar saboda aikata dabi’un ‘yan luwadi

Wata kotu a kasar Masar ta yanke wa wasu mutane hudu hukuncin shekaru takwas a gidan kaso sakamakon samunsu da ta yi da laifin aikata wasu dabi’u da suke kama da na ‘yan luwadi.
An samu mutanen ne da laifin halarta wani bikin farti inda sukai wata shiga cikin tufafin mata, sai kuma laifin caba kwalliya irin ta ‘yan mata. Amma hukuncin na kotun ya janyo kalaman Allah wadai daga kungiyoyin Kare Hakkin Bil’adama da ke kasar.
Inda kungiyoyin suka bayyana cewa tun bayan hanbarar da gwamnatin Muhammad Morsi a cikin watan Julin shekarar 2013 ne, aka fara tsarewa da kuma takura wa mutane ta la’akari da yadda suka bayyana ra’ayoyinsu kan luwadi da madigo.
Idan dai ba a manta ba, wannan hukuncin ba shi ne na farko ba a tarihin kasar ta Masar saboda a cikin shekarar 2001 ma an zartar wa da wasu mutane 52 hukuncin zaman gidan kaso, bayan da aka same su da irin wannan laifin.
A na ta bangaren, babban kungiyar kare Hakkin dan Adam ta kasar ta ce wannan hukunce-hukuncen na yin manuniya ne ga yadda gwamnatin mulkin sojan kasar ke ci gaba da kara danne ‘yancin jama’ar kasar.
A bangare guda kuma, hukuncin na zuwa ne kwana daya bayan wani hukuncin wata kotu inda ta yanke wa wani mutum hukuncin daurin shekaru hudu sakamakon samunsa da laifin shirya wata zanga-zanga ba tare da izinin hukuma ba.