Kotu ta daure tsohon Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy

Sarkozy ya zama tsohon Shugaban Faransa na farko da zai yi zaman gidan yari.

Kotu ta daure tsohon Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy

Tsohon Shugaban Faransa, Nicolas Sarkozy

Wata kotu a kasar Faransa ta yanke wa tsohon Shugaban Kasar, Nicolas Sarkozy hukuncin daurin shekara uku a gidan yari saboda kama shi da laifin rashawa.

Hukuncin da kotun ta yanke wa Sarkozy mai shakara 66 ya sa shi zama Shugaban Faransa na farko da aka daure saboda laifin toshiyar baki.

Kotun ta yake hukuncin ne shari’ar da ake zargin Sarkozy da yin tayin wani aiki mai tsoka ga wani alkali domin samun bayanai kan wani bincike da aka gudanar a kan tsohon shugaban a shekarar 2014 kan badakalar kudaden yakin neman zabe.

Sarkozy ya musanta aikata laifin, yayin da lauyoyinsa ke cewa zai daukaka kara.

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa