Kotu ta daure wanda ya aikata fyade shekara biyu

Kotun Lardi da ke garin Jiwa a yankin Birnin Tarayya, Abuja, ta yanke hukuncin daurin shekara biyu ga wani matashi, bayan ta same shi da laifin kutsawa cikin dakin wata mace mai shekara 22 da ta bar dakinta a bude saboda zafi, sannan ya yi mata fyade. Hakan ya biyo bayan amincewa da tuhumar aikata […]

Kotu ta daure wanda ya aikata fyade shekara biyu
Kotu ta daure wanda ya aikata fyade shekara biyu

Kotun Lardi da ke garin Jiwa a yankin Birnin Tarayya, Abuja, ta yanke hukuncin daurin shekara biyu ga wani matashi, bayan ta same shi da laifin kutsawa cikin dakin wata mace mai shekara 22 da ta bar dakinta a bude saboda zafi, sannan ya yi mata fyade. Hakan ya biyo bayan amincewa da tuhumar aikata laifuffuka biyar ne da matashin mai suna Monday Michael mai shekara 27 ya yi.

Tun farko a yayin gabatar da shi, jami’in ’yan sanda mai gabatar da kara Lawrence Alu na Babban Ofishin ’Yan sanda na garin Gwagwa, Abuja, ya shaida wa kotun cewa, wani makwabcin matashin ne ya kawo kararsa a ofishinsu a ranar 19 ga Maris din nan, bayan ya kutsa cikin dakin makwabciyarsa da misalin karfe 1:00 na dare tare da tursasa mata zuwa wani kango da ke gefen gidan inda ya yi mata fyade. Ya ce laifuffukan sun hada da shiga muhalli ba tare da izinin mai shi ba da kutse da sata da fyade da kuma barazana, wadanda suka saba wa doka ta 342 da ta 347 da ta 288 da ta 282, sai kuma ta 396 na kundin Final Kod.
Ya kuma shaida wa kotun cewa, matashin ya sace wa matar wayarta da kuma Naira 4, 200, sannan ya yi barazanar zai hallaka ta bayan fitowarsa kamar yadda ya furta a lokacin da ake wucewa da shi ofishin ’yan sanda, inji mai shigar da kara.
Da alkalin kotun Mai shari’a Muhammad Lawal Munnir ya waiwaye shi, wanda ake karar ya amince da aikata laifuffukan. Daga nan ne sai alkalin ya yanke masa hukuncin daurin shekara biyu ko zabin biyan tarar Naira dubu 30 a kan laifin aikata fyade, sai kuma daurin wata shida-shida ko zabin biyan tarar Naira dubu biyar ga sauran laifuffuka hudu.