Kotu ta daure wanda ya kama matarsa da kwarto a Amurka
Kotu a Jihar New Jersey da ke Amurka ta daure wani mai suna Sean Donis, har na tsawon shekara 15 a gidan yari, bayan ya bi sawun matarsa da ya gano tana tare da shugaban inda take aiki kuma ya kama su turmi da tabarya. Yadda abin ya faru dai shi ne, shi wannan dan […]

Kotu a Jihar New Jersey da ke Amurka ta daure wani mai suna Sean Donis, har na tsawon shekara 15 a gidan yari, bayan ya bi sawun matarsa da ya gano tana tare da shugaban inda take aiki kuma ya kama su turmi da tabarya.
Yadda abin ya faru dai shi ne, shi wannan dan taliki mai mata wacce ake kira Nancy Donnis ‘yar shekaru 38, ta bukaci mijin ya bata dama za ta tafi wajen liyafar cin abinci da aka gayyace ta.
Wannan ne ya sa ya ba ta dama yayin da shi kuma ya zauna gida domin duba diyarsu ‘yar shekara biyar har lokacin da matar za ta dawo daga inda ta tafi kafin shi kuma ya tafi inda yake son tafiya.
Amma cikin rashin sa’a, suna da ‘yar karamar Kwamfuta (Tablet) wacce yake aiki da ita, sai ya neme ta bai gani ba, amma tana da wata manhajar da za a sa wayar hannu domin gano inda take.
A kokarin hakan, sai ya kunna wannan manhajar domin ta nuna masa inda wannan ‘yar karamar kwamfutar take, sannan ta nuna gidan da matarsa take, a wani bene mai hawa biyu, har cikin dakin da wannan karamar kwamfutar take.
Yana isa kofar ya tura kofar ashe ba a rufe da makullli ba, ko da ya kunna kai ciki sai ya taras da matarsa tare da shugaban ta a wajen aiki mai suna Albert Lopez, dan shekara 58 turmi da tabarya, Nan take sai ya daukesu hoto har sau biyu tare da daukarsu kuma a bidiyo.
Wannan abin ya faru ne a cikin watan Yuli na shekarar 2016. Daga baya wannan mutumin ya samu takarda daga kotu cewa ana tuhumarsa da aikata laifin kutse, shiga gidan mutane ba tare da izini ba, da kuma yi wa mutane shisshigi a cikin harkokinsu.
A cikin watan Satumbar shekarar 2016 ya yi bayyanan farko a gaban alkali a kan wannan tuhumar, inda ya amsa cewa bai yi laifi ba,
Amma shi kuma wanda ya kai kara wato kwarton na Dennis Mista Lopez ya shaida wa kotu cewa sa’ilin da Dennis ya shigo ya sa me shi a halin da ya same su da matarsa, ya umurce shi da ya fita amma yaki. Ya ce idan bai fita ba ya kuka da kansa duk wani abu da ya same shi, amma Lopez ya ce ba zai fita har sai da ya gama daukarsu hoto.
Lopez ya ci gaba da shaida wa kotu cewa tun daga wannan lokacin ya gaza samun sukuni domin kullun ya dawo aiki barci na gagaransa musammam idan ya tuna wannan ranar.
Ya ce kuma matar ta ce masa sun rabu da mijin, abin da ya sa har ya yarda ya fara neman ta ke nan
Dama dai ita matar Dennis tana aiki ne a asibitin Lopez a matsayin mai karbar kudi.
Shi ko lauyan Dennis ya ce ya dace ne a ce an bai wa wanda yake karewa lambar yabo saboda kokarin da ya nuna maimakon ya hau kwarton da bugu ko zagi har ya daure ya dauki hoto, amma ba hukuncin dauri ba.
Sai dai da yake bada hukunci, alkali Nabeela Mcleod ya ce ba shakka Lopez ya sadu da matar Dennis kuma bai yi musu ba, amma dokar shiga gidan mutane bada izini ba tare da shisshigi ga harkokin wasu mutane harma da daukarsu hoto bada yardar su ba sun haifar masa da daurin shekara 15 a gidan yari domin baya da dalilin shiga gidan jama’a bada izni ba, har ya daukesu hoto ya kuma rarraba wa ‘yan uwan matarsa.