Kotu ta daure wanda ya kashe abokinsa shekara 10
Babban Kotun Jihar Adamawa ta yanke wa wani mai Hassan Yahaya daurin shekara 10 a kurukuku kan kashe wani abokinsa mai suna Bapeto Suleiman da ke kauyen Lainde a Karamar Hukumar Shelleng. An kama Hassan Yahaya kan zargin kashe Bapeto ne a shekarar 2014 lokacin da suka fada a kan irin shuka. Shaidu sun bayyana […]
Babban Kotun Jihar Adamawa ta yanke wa wani mai Hassan Yahaya daurin shekara 10 a kurukuku kan kashe wani abokinsa mai suna Bapeto Suleiman da ke kauyen Lainde a Karamar Hukumar Shelleng.
An kama Hassan Yahaya kan zargin kashe Bapeto ne a shekarar 2014 lokacin da suka fada a kan irin shuka.
Shaidu sun bayyana wa kotun cewa lokacin da marigayin ya sayi ’ya’yan itatuwa da ake kira da Bousbous sai ya rika ci shi da abokansa sannan yana zuba irin a leda sannan kuma wasu na zuba a kasa.
Sai Hassan ya shiga tsince wadanda suke zuba a kasa da burin shi ma zai shuka sai marigayin ya hana shi tsintar na kasan hakan ya janyo fada a tsakaninsu wanda ya sa marigayin ya ciro wuka ya daba wa abokinsa Hassan shi ma Hassan ya ciro tasa ya daba masa wanda hakan ta yi sanadiyar mutuwar Bapeto.
Alkalin Koyun Mai shari’a Abdul’azeez Waziri ya yanke wa Hassan hukuncin daurin shekara 10.
Sannan ya gargade shi kan ya zama mutumin kirki kuma ya kaurace wa fadace-fadace.