Kotu ta daure wani tsoho kan lalata da ’yar shekara 4 a Jigawa

Babbar Kotun Majistare ta Kafin Hausa a Jihar Jigawa ta daure wani tsoho mai shekara 57 mai suna Malam Ya’u mai sana’ar gyaran tantan dan asalin karamar Hukumar Kirikasamma bisa samunsa da laifin lalata da wata yarinya ’yar shekara hudu (an sakaye sunanta) a Unguwar Tambirawa a garin Kafin Hausa. An shaida wa kotun cewa […]

Kotu ta daure wani tsoho kan lalata da ’yar shekara 4 a Jigawa
Kotu ta daure wani tsoho kan lalata da ’yar shekara 4 a Jigawa

Babbar Kotun Majistare ta Kafin Hausa a Jihar Jigawa ta daure wani tsoho mai shekara 57 mai suna Malam Ya’u mai sana’ar gyaran tantan dan asalin karamar Hukumar Kirikasamma bisa samunsa da laifin lalata da wata yarinya ’yar shekara hudu (an sakaye sunanta) a Unguwar Tambirawa a garin Kafin Hausa.

An shaida wa kotun cewa tsohon ya yi amfani da Naira 10 ya yaudari yarinyar a lokacin da take wasa a kofar gidansu ya ce ta sayi rake ita da ’yan uwanta da yarinyar ta saki jiki da shi, sai ya dauke ta ya yi lalata da ita. Kuma yana cikin lalata da ita ce wasu matasan unguwar da suka jima suna fakonsa bisa zargin lalata da kananan yara suka kama shi inda suka iske ya bata tabarmar da yake zaune a kai.
Wani mazaunin unguwar mai suna Adamu Ibrahim ne ya sanar da ’yan sandan Kafin Hausa lamarin, kuma suka kama wanda ake tuhumar suka gurfanar da shi a gaban kotu.
Wanda ake zargin ya amsa laifinsa, inda ya shaida wa kotun cewar ya dade yana aikata irin wannan laifi kuma abin da ya rabo shi da karamar hukumarsu ta ke nan, kuma ya roki kotun ta yi masa sassauci.
Da yake zartar da hukuncin, Alkalin Kotun Mai shari’a Abubakar Jibrin ya ce kotun ta daure mai laifin shekara hudu a gidan yari ba tare da zabin biyan tara ba kuma zai biya iyayen yarinyar diyyar Naira dubu 10, kamar yadda sashi na 285 na Final Kod ya tanada.
A wata sabuwa Dagacin Balangu da ke masarautar Hadeja Alhaji Ibrahim Shehu ya warware rawani wani mai unguwa da ke cikin garin Bulangu saboda zarginsa da lalata da wata yarinya ’yar makaranta da aka sakaya sunanta
Alhaji Ibrahim Shehu ya ce warware rawanin Malam Umaru Chore mai unguwar Jarma Bulangu abu ne da ya zama dole saboda an jima ana zarginsa da aikata haka, ya ce tuni ya sanar da fadar Mai martaba Sarkin Hadeja kuma ta amince da matakin.
Ya ce sauke mai unguwar ne ya hana iyayen yarinyar kai mai unguwar kotu ko gaban jami’an tsaro don neman hakkin ’yarsu, saboda hukuncin da masarautar Hadeja ta dauka kan mai unguwar ya gamsar da su.

KADVS ta daƙile yunƙurin sace yara da ceto wasu a Zariya

Gwamnatin Tinubu na yunƙurin hana ni yin takara — Peter Obi

An gurfanar da ƙarin mutum 17 bisa zarginsu a kisan malama

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi