Kotu ta dawo da Sarkin Kontagora kan kujerarsa

Tsugune ba ta kare ba a rikicin kujerar Sarkin Kontagora na bakwai.

Kotu ta dawo da Sarkin Kontagora kan kujerarsa

Mohammed Barau Kontagora, Sarkin Kontagora

Kotu da mayar da Sarkin Kontagora, Alhaji Mohammed Barau, da aka dakatar a kan kujerarsa.

A zaman Babbar Kotun da ke zamanta Minna na ranar Laraba, ta soke  umarninta na farko da ya hana Alhaji Mohammed Barau gabatar da kansa matsayin Sarkin Sudan Kontagaro na Bakwai.

Tun da fakro kotun ta ba da umarnin ne bayan wasu mutum 15 da suka tsaya takarar neman sarautar sun kai mata kara suna kalubalantar ba shi sarautar da Gwamnatin Jihar Neja ta yi.

Lauyoyin mutum uku na farko daga cikin masu karar sun bayyana wa kotun cewa kujerar sarautar Sarkin Kontagora na da matukar muhimmaci,  don haka bai dace a bar ta babu kowa a kanta ba, musamman idan aka yi al’akari da yanayin tsaro a jihar da ke bukatar gudummawar sarakunan gargajiya ta hanyar tattaunawa da mabiyansu.

Sun kara da cewa Masarautar Kontagora babbar masarauta ce da ta hada kananan hukumomi shida, saboda haka bai kamata a bar ta babu sarki ba.

A karar da suka shigar, sun bukaci kotun ta hana Alhaji Mohammed Barau Kontagora gabatar da kansa a matsayin Sarkin Kontagora na bakwai; Sannan ta hana Gwamnatin Jihar Neja mika mishi sandar sarauta.

Bayan sauraron jawabansu, alkalin kotun, Mai Shari’a Abdullahi Mikailu, ya jingine umarnin da ya bayar da farko da ya sauke Alhaji Mohammed Barau daga kujerar Sarkin Kontagora, sannan ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar 11 ga watan Nuwamba 2021.

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50 a Kaduna

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54