Kotu ta garkame mata biyu a gidan yari saboda bara da yara
Wata kotu a Legas, ta garkame wasu mata biyu a gidan kaso saboda laifin yaudarar jama’a, yayin da suka nade jikin wasu kananan yara da bandeji domin yin badda-kama suna yawon bara da su. Matan masu suna Amarachi Eke da Chioma Eze, an yanke wa kowacensu hukuncin daurin wata 2 a jarun da tarar Naira […]

Wata kotu a Legas, ta garkame wasu mata biyu a gidan kaso saboda laifin yaudarar jama’a, yayin da suka nade jikin wasu kananan yara da bandeji domin yin badda-kama suna yawon bara da su. Matan masu suna Amarachi Eke da Chioma Eze, an yanke wa kowacensu hukuncin daurin wata 2 a jarun da tarar Naira dubu 5 a kan haka.
Asirin matan ya tonu ne a wurare biyu daban-daban. An kama Chioma da yaro mai shekaru 9, wanda take cewa danta ne, a kan titin Ajose Adeogun da ke bictoria Island a Legas, inda wani ma’aikacin hukumar tsaftace muhalli mai suna Betty Albert, ya tausaya ya fita daga motarsa domin a kai yaron asibiti a yi masa magani amma sai Chioma, ta umarci yaro ya gudu. Wajen gudun ne, sai ya fada hannun ’yan sanda, wadanda suka yi binciken kwakwaf suka cire filasta da bandeji da aka daura a ciki da kwaurin yaron suka ga lafiyarsa lau, babu ciwo a jikinsa.
Ita kuwa Amarachi, an cafke ta ne a kusa da Eko Hotel, tana tare da danta mai shekaru 6, wanda ta nannade jikinsa da bandeji a matsayin mara lafiya tana neman kudi da shi.
Wata majiyar ’yan sanda ta shaida wa wakilinmu cewa, bincike ya nuna matan ba su ne ainihin iyayen yaran ba, iyayensu na hakika, suna zaune ne a garin Awka a Jihar Anambra, a inda Chioma da Amarachi suka yi musu karyar za su tafi da ’ya’yansu zuwa Legas ne domin sanya su a makarantu da za su sami ingantaccen ilmin zamani.
Alkalin Kotun Iyali na 1 da ke Yaba, a Legas, Mai Shari’a Y.O. Aje-Afunwa ya ce ya yanke wannan hukunci ne domin ya zama darasi gare su, domin idan sun kammala zaman jarun su samu halastacciyar hanyar samun abin kansu, maimaikon wannan mummunar hanya.
Mai ba Gwamnan Jihar Legas shawara ta musamman a kan harkokin matasa da kyautata rayuwa, Dokta Dolapo Badru, a tsokancinsa, ya nuna takaici da mamakin ganin irin wannan lamari na neman kudi.
Ya ce gwamnatin Jihar Legas, za ta ci gaba da daukar tsauraran matakan dakile irin wadannan dabi’u a tsakanin jama’a, kuma ya nuna cewa wannan mummunar hanya ce da rashin tausayi wajen gurbata rayuwar kananan yara.
A karshe ya yi fatan hukunci zai zama darasi ga masu sha’awar aikata irin wannan danyen aikin.