Kotu ta hana EFCC kama Kwankwaso

Kotun ta bayar da umarnin ne, bayan da ƙarar da Kwankwaso da wasu suka shigar gabanta.

Kotu ta hana EFCC kama Kwankwaso

Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar NNPP a zaben 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Wata Babbar Kotu da ke Sakatariyar Audu Baƙo a Jihar Kano, ta bayar da umarnin hana Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arziƙi Zagon Ƙasa (EFCC), kama, gayyata ko muzgunawa jagoran jami’yyar NNPP na ƙasa, Rabiu Musa Kwankwaso da wasu mutane bakwai.

Waɗanda suka shigar da ƙarar su ne, NNPP, Dokta Ajuji Ahmed, Dipo Olayanku, Ahmed Balewa, Cif Clement Anele, Lady Folshade Aliu, Injiniya Buba Galadima da kuma Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Wadda ake ƙara ita ce Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arziƙi Zagon Ƙasa (EFCC).

Mai shari’a Yusuf Ubale Muhammad, ya bayar da umarnin ne, a lokacin da ya karanta t ƙarar da aka shigar a ranar 5 ga watan Yuni, 2024.

Ya ce, “An bayar da umarni na wucin gadi, wanda ke hana wadda ake ƙara, ko wasu jami’anta kama ko gayyatar waɗanda suka shigar da ƙara.”

Kotun ta ɗage shari’ar zuwa 24 ranar ga watan Yuni, 2024 domin ci gaba da sauraron ƙarar.

Idan ba a manta ba EFCC ta fara farautar tsohon gwamnan na Kano kan zargin karkatar da kuɗaɗen ’yan fansho.

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta