Kotu ta hana FRSC tare motoci a titunan Kano
Mai Shari’a M. S. Shuaibu ne ya yanke hukuncin bayan ƙarar da lauya, Abba Hikima ya shigar.
Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta hana jami’an Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) tsayar da masu ababen hawa a titunan cikin Jihar Kano ba tare da umarnin doka ba.
Mai Shari’a M. S. Shuaibu ne ya yanke hukuncin bayan ƙarar da lauya, Abba Hikima ya shigar.
Inda ya ce matakin da jami’an FRSC suka ɗauka na tsayar da motoci da tambayar direbobi a wasu titunan cikin birnin Kano ya saɓa wa ’yancin walwala da zirga-zirgar da Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya tanada.
Kotun ta kuma umarci Hukumar FRSC ta wallafa ba da haƙuri a wata jarida ta ƙasa tare da biyan mai ƙarar Naira 800,000 a matsayin diyya da kuɗin shari’a.