Kotu ta hana Hukumar EFCC kama tsohon Gwmanan Jigawa

Babbar Kotun Tarayya da ke Dutse fadar Gwamnatin Jihar Jigawa Dutse, a zaman da ta yi ranar Litinin da ta gabata ta umarci hukumar yaki da yi wwa tatttalin arziki ta’annati ta “EFCC” da ta dakatar da kudirinta na kama tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Ibrahim Saminu Turaki bisa zargin sama da fadi da dukiyar […]

Kotu ta hana Hukumar EFCC kama tsohon Gwmanan Jigawa
Kotu ta hana Hukumar EFCC kama tsohon Gwmanan Jigawa

Babbar Kotun Tarayya da ke Dutse fadar Gwamnatin Jihar Jigawa Dutse, a zaman da ta yi ranar Litinin da ta gabata ta umarci hukumar yaki da yi wwa tatttalin arziki ta’annati ta “EFCC” da ta dakatar da kudirinta na kama tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Ibrahim Saminu Turaki bisa zargin sama da fadi da dukiyar jiharsa, a lokacin da yake kan karagar mulki.

Kwanan baya ne Hukumar EFCC tk bayar da cigiyar tsohon Gwmanan Jihar Jigawa, inda ta yi nuni da cewa, tana nemansa ruwwa a jallo.
Don haka lauyan tsohon gwamnan ya garzaya Babbar Kotun Tarayya tunda a baya kotun ta dakatar da batun kama tsohon gwamnan, bisa tuhumar da ake yi masa, saboda rashin bayyanar wadanda suka yi kararsa a gaban kotun, tare da gazawar su na gabatar da shaidu, don haka kotun ta kori karar daga gabanta.
Lauyan tsohon gwamnan ya bukaci kotun ta kare martabar tsohon gwamnan, shi ya sa mai shari’a, Sabiu Yahuza ya umarci hukumar ta EFCC da ta dakatar da yunkurinta na kama tsohon gwamnan, har zuwa watan biyu na sabuwar shekara, inda kotun za ta zauna domin nazarin hukuncin da ya dace.
Kotun ta umarci bangarorin biyu da shi lauya mai kare tsohon gwamnan, da hukumar EFCC da su hakura, su ajiye makamansu zuwa ranar 4/2/2015, ranar da kotun za ta sake zama domin sauraren karar.
Duk da wannan matsaya da aka dauka, lauyan tsohon gwamnan, Barista Sa’idu Tudun Wada ya bukaci kotun da ta yi watsi da karar, ya kuma soki lamirin hukumar EFCC da cewar tana yin hakan ne domin bata wa tsohon gwamnan suna.