Kotu ta hana Khalid Diso kiran kansa Shugaban Karamar Hukumar Gwale
Babbar kotun Jihar Kano ta hana Khalid Ishaq Diso gabatar da kansa a matsayin shugaban karamar hukumar Gwale.
Babbar kotun Jihar Kano ta hana Khalid Ishaq Diso gabatar da kansa a matsayin shugaban karamar hukumar Gwale.
Umarnin wucin gadi da alkalin kotun, Mai shari’a Aisha Ibrahim Mahmoud ta bayar bisa bukatar da lauyan masu kara, Barista Bala Nomau ya gabatar ya kuma hana Khalid Ishaq Diso da ma kowa daga gabatar da kansa matsayin shugaban karamar hukumar har sai an saurari karar da ke gaban kotu.
Tun da farko dai karamar hukukumar ta sanar da kotun cewa, kwamitin da majalisar dokokin jihar Kano ta kafa ya tsawaita wa’adin dakatarwar da aka yi wa Khalid saboda zargin amfani da matsayinsa yadda bai dace ba.
Wadanda suka shigar da karar su ne Ghali Nalele Bature da Ghali Umar Diso, yayin da wadanda ake karar sun hada da Khalid Ishaq Diso, ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar Kano, da majalisar dokokin jihar Kano, da kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano, da kuma karamar hukumar Gwale.
Kotun ta dage sauraren karar zuwa ranar 5 ga watan Junairu, 2024.