Kotu ta hana sake gurfanar da Uzo Kalu
Babbar Kotun Tarayya ta hana hukumar EFCC sake gurfanar da tsohon Gwamnan Jihar Abin, Orji Uzo Kalu, kan zargin badakalar Naira biliyan 1.7 da a baya aka daure shi a gidan yari a kai. Mai Shari’a Inyang Ekwo ne ya ba da umarnin yayin sauraron karar da Mista Kalu ya shigar yana neman kotun ta […]
Babbar Kotun Tarayya ta hana hukumar EFCC sake gurfanar da tsohon Gwamnan Jihar Abin, Orji Uzo Kalu, kan zargin badakalar Naira biliyan 1.7 da a baya aka daure shi a gidan yari a kai.
Mai Shari’a Inyang Ekwo ne ya ba da umarnin yayin sauraron karar da Mista Kalu ya shigar yana neman kotun ta hana sake gurfanar da shi, wanda ya ce tamkar maimaicin abin da aka yi a baya ne, alhali har an sako shi daga gidan yari.
Alkalin kotun ya ce babu wani dalili ko umarnin kotu da zai sa a sake gurfanar da tsohon gwamnan.
A cewarsa, umarnin sake gurfanarwa da Kotun Koli ta bayar bai shafi Uzo Kalu ba.
Amma ya ba da izinin sake gurfanar da Kwamishinan Kudi, Jones Udeogwu, wanda a shari’ar da aka yi a baya aka kama da laifi tare da Kalu.