Kotu ta hana ’yan kwadago tafiya yajin aiki kan janye tallafin mai
Ranar Laraba dai ‘ya kwadagon suka shirya shiga yajin aikin
Kotun Ma’aikata ta Tarayya ta dakatar Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) daga yunkurinta na fara yajin aiki ranar Laraba saboda janye tallafin man fetur.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Olufunke Anuwe ce ta bayar da umarnin ranar Litinin.
- Ma’aikatan shari’a za su tsunduma yajin aiki kan janye tallafin mai
- ’Yan ta’addan ISWAP 82 sun nitse a ruwa suna kokarin tsere wa sojoji
Kotun dai ta hana NLC da duk kungiyoyin da ke karkashinta ci gaba da shirye-shiryen fara yajin aikin ranar 7 ga watan Mayun 2023, har sai ta kammala sauraro da kuma yanke hukunci kan ainihin karar.
Kotun ta umarci sauran wadanda ake karar a cikin shari’ar da ma kungiyar ta NLC da kada su dauki wani mataki har zuwa ranar zaman kotun na gaba ranar 19 ga watan Yuni.
Hukuncin kotun dai ya biyo bayan wata kara da ofishin Babban Lauyan Gwamnati kuma Minstan Shari’a ya shigar yana neman a hana ’yan kwadagon shiga yajin aiki.
NLC dai ta ayyana yunkurinta na fara yajin aiki a duk fadin Najeriya daga ranar Laraba, bayan Gwamnatin Tarayya ta bakin Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL) ta sanar da yin karin kudin mai har zuwa sama da N500.
Matakin kuma ya biyo bayan kalaman Shugaban Kasa Bola Tinubu lokacin da aka rantsar da shi a ranar Litinin, lokacin da ya sanar da cire tallafin mai gaba daya.