Kotu ta hana ’yan sanda sake taɓa Muhuyi Rimingado
Babban Kotun Jihar Kano ta rundunar ’yan sanda sake kamawa, gayyata ko tsare Shugaban Hukumar Yaƙi da Rashawa da Karɓar Ƙorafe-ƙorafe ta Jihar Jihar Kano (PCACC). Magaji Rimingado.
Babban Kotun Jihar Kano ta rundunar ’yan sanda sake kamawa, gayyata ko tsare Shugaban Hukumar Yaƙi da Rashawa da Karɓar Ƙorafe-ƙorafe ta Jihar Jihar Kano (PCACC), Magaji Rimingado.
Kotun ta ba a da umarnin ne bayan ƙarar da Babban Lauyan jihar Kano da hukumar PCACC da kuma Magaji Magaji Rimingado suka shigar.
Waɗanda ake ƙara su ne rundunar ’yan sandan Najeriya, Sufeto-Janar na ’yan sanda da Mataimakinsa Ma kula da Shiyya ta Ɗaya da Kwamishinan ’Yan Sanda Kano da ASP. Ahmed M. Bello da Bala Muhammad Inuwa.
Kotun ta ɗage shari’ar zuwa ranar 2 ga watan Fabrairu, 2025.
A ranar Juma’a ’yan sanda sun kama shugaba na hukumar da yamma, inda suka tsare shi na tsawon awanni, daga baya ba da belinsa da tsakar dare, tare da umartar sa ya kai kansa hedikwatar rundunar da ke Abuja ranar Litinin don amsa tambayoyi.