Kotu ta hana yin zaɓen ƙananan hukumomin Kano
Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kano ta dakatar da Hukumar Zaben Jihar Kano daga gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi.
Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kano ta dakatar da Hukumar Zabe ta Jihar Kano (KANSIEC) daga gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi.
Mai Shari’a Simon Ameboda ya kuma umarci Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) kada ta ba wa KANSIEC kayan zabe.
Umarnin kotun na zuwa ne a ranar Talata, a yayin da hukumar KANSIEC ke shirin gudanar da zaben a rana Asabar.
Da take yanke hukuncin, kotun ta bayyana cewa nadin mambobin Jam’iyyar NNPP a matsayin jami’an hukumar ya saba wa kundin tsarin mulkin Nijeriya da kuma dokar hukumar.
Ta kara da cewa, don haka babu yadda za a yi KANSIEC ta gudanar da zaben a yadda take a yanzu, sai an sauya nade-naden da ke hukumar.