Kotu ta haramta ‘ayyukan’ kungiyar Ikhwanul Muslimina a Masar
Wata kotu a kasar Masar ta haramta “dukkan ayyukan” kungiyar Ikhwanul Muslimina. Kotun Muhimman Al’amura ta Alkahira ta ce wannan hukuncin ya shafi ita kanta kungiyar ta Musulunci da kungiyoyin bayar da tallafinta da duk wasu kungiyoyi da suke karkashinta. Kuma ta umarci gwamnatin rikon kasar ta kwace kudaden kungiyar Ikhwanu, kuma ta kafa wata […]
Wata kotu a kasar Masar ta haramta “dukkan ayyukan” kungiyar Ikhwanul Muslimina. Kotun Muhimman Al’amura ta Alkahira ta ce wannan hukuncin ya shafi ita kanta kungiyar ta Musulunci da kungiyoyin bayar da tallafinta da duk wasu kungiyoyi da suke karkashinta.
Kuma ta umarci gwamnatin rikon kasar ta kwace kudaden kungiyar Ikhwanu, kuma ta kafa wata hukuma da za ta kula da kadarorin kungiyar zuwa lokacin da za a saurari wata daukaka kara kan hukuncin.
Mahukuntan sojan kasar sun kaddamar da yunkurin karya kungiyar tun bayan juyin mulki ga Shugaba Mursi a ranar 3 ga Yulin da ya gabata.
dimbin manyan jami’anta ciki har da babban murshidinta Mohammed Badie suna tsare bisa tuhumar tunzura jama’a su tayar da rikici da kuma kisan kai.
Sojoji wadanda suke nuna kamen da suke yi ga jama’a a matsayin fafatawa da “ta’addanci” sun kashe daruruwan jama’a masu zanga-zangar neman a mayar da Mursi kan kujerarsa wadanda galibinsu magoya bayan Ikhwanu ne.
kungiyar Ikhwanu mai shekara 85, shugabannin gwamnatin soja sun taba haramta ta a 1954, amma aka yi mata rajista a matsayin kungiyar bada taimako da aka sanya mata suna kungiyar Muslim Brotherhood Association a watan Maris sakamakon wata shari’a a kotu da abokan gabanta ke tuhumar matsayinta a karkashin doka.
Ikhwanu ta kuma yi rajistar bangaren siyasarta ta zama Jam’iyyar Freedom and Justice Party (FJP), wadda aka kafa ta a shekarar 2011 a matsayin jam’iyya bayan juyin juya-halin da ya kawar da tsohon Shugaban Masar Hosni Mubarak.
Bayan juyin mulki da aka yi wa Mursi da kuma jingine tsarin mulkin kasar mai alaka da Musulunci na shekarar 2012, an ba kotun tafiyar da al’amuran Alkahira da Ma’aikatar Kula da Jin Dadin Jama’a alhakin sake duba matsayin Ikhwanu a karkashin doka.
Hukuncin kotun na ranar Litinin ya haramta ita kanta Ikhwanu da kungiyarta mai zaman kanta (NGO) da “duk wata cibiya da aka cisgo daga jikinta ko take da alaka da Ikhwanu,” ko “karbar tallafin kudi daga gare ta.” Sai dai babu bayani kan ko ya shafi ayyukanta na jin kai da na taimakon jama’a da take gudanrwa ciki har da makarantu da asibitoci.
Wani babban dan Ikhwanu, Ibrahim Mounir ya bayyana hukunci da “tsabagen kama-karya,” inda ya ce wannan ba zai sa kungiyar ta bace daga bayan kasa ba.
Ya ce, “Za ta ci gaba da kasancewa da taimakon Allah ba da dokar kotun al-Sisi ba,” yana gaya wa gidan talabijin na Mubashir Misr na Aljazeera.
Kotun ba ta bayyana dalilin yanke wannan hukunci ba, sai dai ta yi hakan ne kan karar da wata jam’iyya mai ra’ayin mazan-jiya ta National Prograssibe Unionist Party da aka fi sani da Tagammu ta kai, tana zargin Ikhwanu da kasancewa “ta ta’adda” kuma “tana amfani da addini a harkokin siyasa.”
Dama an ruwaito Ministan Jin Dadin Jama’a Ahmed al-Borai yana cewa zai rusa kungiyar taimakon jama’a ta Ikhwanu (NGO), inda ya shaida wa gidan talabijin na Dream Tb a ranar Asabar cewa nan ba da jimawa ba zai buga bayanin da za su nuna dalilansa.