Kotu ta haramta nadin manyan hafsoshin Najeriya

Wata kotu a Abuja ta bayyana nadin dukkan manyan hafsoshin sojan Najeriya a matsayin haramtacce saboda bai samu amincewar Majalisar Dattawa ba kamar yadda tsarin mulki ya tanada.Alkalin Babbar Kotun Tarayya Mai shari’a Adamu Bello ne ya yanke wannan hukunci a ranar Litinin da ta gabata, inda ya haramta wa Shugaban kasa sake nada irin […]

Kotu ta haramta nadin manyan hafsoshin Najeriya
Kotu ta haramta nadin manyan hafsoshin Najeriya

Wata kotu a Abuja ta bayyana nadin dukkan manyan hafsoshin sojan Najeriya a matsayin haramtacce saboda bai samu amincewar Majalisar Dattawa ba kamar yadda tsarin mulki ya tanada.
Alkalin Babbar Kotun Tarayya Mai shari’a Adamu Bello ne ya yanke wannan hukunci a ranar Litinin da ta gabata, inda ya haramta wa Shugaban kasa sake nada irin wadannan mukamai ba tare da amincewar Majalisar Dattawa ba. Ya yanke wannan hukunci ne kan karar da wani lauya dan rajin kare hakkin dan Adam Festus Keyamo ya kai a shekarar 2008, wanda ya nemi kotun ta bayyana nadin a matsayin ya saba wa tsarin mulki, haram ne kuma batacce rusasshe saboda bai samu amincewar Majalisar Dokoki ta kasa ba.
Keyamo ya roki kotun ta yanke hukunci kan ko fassarar tanade-tanaden Sashi na 218 na Tsarin Mulkin 1999 da Sashi na 18 na Dokar Rundunar Soja mai lamba Cap. A.20, ta dokokin Najeriya na shekarar 2004, Shugaban kasa zai iya nada Babban Hafsan Sojan Sama da Babban Hafsan Sojan kasa da Babban Hafsan Sojan Ruwa ba tare da abbatarwa daga Majalisar Dokoki ta kasa ba.
A hukunacinsa Mai shari’a Bello, ya ce, Shugaban kasa ba ya da wannan iko, don haka ya amince da dukkan bukatun Keyamo.
Da Fadar Shugaban kasa ke maida martani kan hukunci ta ce, tana jirar shawarar Ma’aikaar Shari’a kan matakin da za ta dauka a gaba. Kakakin Shugaban kasa Reuben Abati ya shaida wa wakilinmu a tarho cewa, “Ban karanta hukuncin ba, kuma ba zan ce komai kan hukuncin da ba karanta ba. Kuskure ne ka yi sharhi kana bin da ke shafi jaridu. Amma ina ba ka tabbacin Ma’aikatar Shari’a za ta nazarci hukuncin kuma a shawarci gwamnati yadda ya kamata kan maakin dauka. Amma yanzu abin da zan iya cewa ke nan.”
Kakakin Majalisar Dattawa Sanata Eyinnaya Abaribe (PDP Abiya) ya ce majalisar ba ta ga kwafen hukuncin ba, don haka ba zai ce komai a kai ba. “Lokacin da Majalisar ta samu kwafen za mu mika wa kwamitocinta na shari’a da sauransu don neman shawara, bayan nan ne za mu yyi bayani da daukar mataki na karshe a kai,” inji Abaribe.
Hukuncin kotun ya sa ayar tambaya kan makomar mukaman Babban Hafsan Tsaro Admiral Ola Sa’ad Ibrahim da Babban Hafsan Sojan kasa Janar Azubuike Ihejirika da Babban Hafsan Sojan Sama Iya Mashal Aled Badeh da kuma Babban Hafsan Sojan Ruwa Admiral Dele Ezeoba.