Kotu ta haramta wa kare yin haushi da daddare a kasar Croatia

Wani makwabcin mai kare, Anton Simunobic ya samu amincewar kotu na haramta wa Karen makwacinsu yin haushi da daddare, saboda yana cutar da lafiyarta.Wannan makwafci da ke zaune a wani kauyen kasar Croatia ya samu izinin kotun ne, inda aka bayyana haramcin haushin Medo a cikin dare. Idan kuma mai Karen, wato Anton Simunobic ya […]

Kotu ta haramta wa kare yin haushi da daddare a kasar Croatia
Kotu ta haramta wa kare yin haushi da daddare a kasar Croatia

Wani makwabcin mai kare, Anton Simunobic ya samu amincewar kotu na haramta wa Karen makwacinsu yin haushi da daddare, saboda yana cutar da lafiyarta.
Wannan makwafci da ke zaune a wani kauyen kasar Croatia ya samu izinin kotun ne, inda aka bayyana haramcin haushin Medo a cikin dare. Idan kuma mai Karen, wato Anton Simunobic ya ki amincewa, to zai biya tarar Dala dubu uku da 160.
Yanzu dai an killace wannnan kare dan shekara uku a wani rumbun hatsi, inda yake zama daga takwas na safe zuwa takwas na dare, ta yadda ba za a bar shi ya yi ta kai kawo ba. Wannan kare Medo, shi kadai ne Karen da aka haramta wa yin haushi a kasar Croatia.
Wannan kara da aka kai Medo kan cewa yana cutar da lafiyar makwaciyar ubangidansa, maigida Simunobic ya ce ‘karya ne.’
“Yana yin haushi kamar kowane irin kare,” a cewar Simunobic. “Ya kan yi haushin idan ya ga kyanwa, ko wani mutumin da bai snai ba, idan ya shigo harabar inda yake,” inji shi.
Wannan mawuyacin hali da aka sanya Medo ta sanya ya samu dimbin magoya baya, wadanda suka bude shafin sadarwa na facebook, inda suke nuna goyon bayansu ga Medo, har ta kai ga labarinsa ya ja hankalin al’umma a cikin wannan shekara. Masu karnuka da dama sun aike da hotunan akrnukansu don nuna goyon bayansu ga wannan kare, kai har ma masu maguna sun shiga jerin amsu nuna goyon baya ga kare Medo.
Har yanzu kotun garin Pula ba ta yanke hukunci na karshe ba, inda wannan makwafciya ke neman diyyar Yuro Dubu da 400.