Kotu ta haramta wa miji magana da matarsa na tsawon mako 2

Alkalin kotu daga karshe ya bayar da belinsa a kan Naira 50,000.

Kotu ta haramta wa miji magana da matarsa na tsawon mako 2

Kotu

Wata Kotu Majistare a Ado Ekiti fadar Jihar Ekiti ta haramta wa wani mutum yin magana da matarsa na tsawon mako biyu har sai sun sake dawowa kotun ranar da za ta sake zama.

Babban Majistare Dolamu Babalogbon ne ya bayar da umarnin ga mijin matar mai suna Chibuke Nwakedi mai shekara 43 inda ya haramta masa yi mata magana baka-da-baka ko ta waya sai dai ta hanyar wani a tsakani ko kuma ta hanyar magana da lauyanta.

A yayin gabatar da karar mai gabatar da kara Sufeton ’Yan sanda Sodik Adeniyi ya shaida wa kotun cewa wanda ake kara a ranar 3 ga watan Maris din nan da misalin karfe 8:00 na dare ya doki matarsa mai suna Blessing Nwokedi inda ya buga kafarta da gadon katako wanda hakan ya jawo mata targade.

Wanda ake karar kuma a wannan lokaci ya yi kokarin tayar da husuma wanda haka na iya kaiwa ga tashin hankali kuma hakan ya saba wa doka da za a iya hukunta shi a bisa tanadin sassa na 186 da 181 na Kundin Manyan Laifuffuka na jihar na shekara 2021.

Lauyan wanda ake kara Barista Gbenga Aribiyi na roki kotun ta bayar belin wanda ake kara yana mai alkawarin ba zai gudu ba kuma zai gabatar da masu tsaya masa nagartattu.

Alkalin kotu daga karshe ya bayar da belinsa a kan Naira 50,000 da tare da kawo masu tsaya masa mutum biyu da za su ajiye wannan kudi sannan ya daga ci-gaba da sauraron karar zuwa 28 ga wannan wata.