Kotu Ta Haramta wa Murja Kunya Amfani Da Soshiyal Midiya

An bai wa Kwamishinan ’Yan sanda umarnin bibiyar Murja don ganin ba ta yi wallafa ko wani irin saƙo a soshiyal midiya ba.

Kotu Ta Haramta wa Murja Kunya Amfani Da Soshiyal Midiya

Babbar Kotun Jihar Kano da ke zamanta a Bompai ta haramta wa fitacciyar jarumar nan ta TikTok Murja Ibrahim Kunya amfani da soshiyal midiya.

Wannan dai na zuwa ne a yayin da kotun karkashin jagorancin Mai shari’a Nasiru Saminu ta bayar da belin Murja Kunya kan kuɗi Naira dubu ɗari biyar.

Daga cikin sharuɗan beli da kotun ta gindaya wa jarumar, an buƙaci ta kawo mutane biyu da za su tsaya mata, kuma dole ɗaya daga ciki ya kasance dan uwanta na kusa yayin da ɗayan zai kasance wanda ya mallaki kasa mai daraja a Jihar Kano.

Kazalika, kotun ta kuma hana Murja Kunya sanya duk wani sako ko yin martani a kafafen sada zumunta na zamani kamar su TikTok da Facebook da Instagram da sauransu har na tsawon lokacin da za ta kasance karkashin zaman beli.

Dangane da hakan ne kotun ta umarci Kwamishinan ‘Yan sandan Kano da ya riƙa bibiyar halin da jarumar ke ciki don ganin ba ta saba wa haramcin amfanin amfani da kafafen sada zumuntar ba.

Wakiliyarmu ta ruwaito cewa, kotun ta halasta wa kwamishinan ’yan sandan kama jarumar tare da gaggauta miƙa ta gaban kotu da zarar an same ta da ƙetare iyakar haramcin amfaninda zaurukan na sada zumunta.

Kotun ta kuma bayar da umarni ga Hukumar da ke kula da Asibitocin Jihar Kano da Asibitin Kula da Kwakwalwa na Gwamnatin Tarayya da ke Dawanau su kawo wa kotun rahoton gwajin kwakwalwar Murja a cikin kwanaki bakwai.

Idan za a iya tunawa, tun a makonnin da suka gabata fitacciyar jarumar ta TikTok Murja Ibrahim Kunya ta shigar da ƙara gaban kotun tana kalubalantar Babban Mai shari’a na Jihar.

A ƙunshin ƙarar da ta shigar tana neman a yi mata tsakani da su, Murja ta haɗa da Alkalin Kotun Shari’ar Musulunci, Nura Yusuf Ahmad da Kwamishinan ‘Yan sandan Kano da Hukumar Hisbah ta Jihar Kano da Hukumar da ke kula da Asibitocin Jihar Kano da Asibitin Kula da Masu lalurar kwakwalwa na kasa da ke Dawanau.

Takardar ƙarar tun a wancan lokacin ta nuna cewa, Babbar Kotun ta cimma muradu huɗu daga cikin jerin buƙatu bakwai da lauyoyin Murja suka gabatar wa Mai Shari’a Nasiru Saminu.

Sai dai Aminiya ta lura cewa, daga cikin buƙatun lauyoyin Murja da kotun ta yi watsi da su, har da ta neman mayar wa wadda suke wakilta wayarta ta hannu kirar iPhone da kuma katin banki na ATM.

Haka kuma Murja ta nemi kotun da ta sanya Asibitin Muhammad Abdullahi Wase da Asibitin Kula da Kwakwalwa na Gwamnatin Tarayya da ke Dawanau su ba lauyoyinta rahoton gwajin kwakwalwarta.

Aminiya ta ruwaito cewa, bayan karanta sharuɗan belin a zaman kotun na ranar Litinin, alkalin kotun ya ɗage sauraren shari’ar zuwa ranar 16 ga Mayun 2024.

Ana iya tuna cewa, a bayan nan dai Mai Shari’a Malam Nura Yusuf Ahmad na Kotun Shari’ar Musulunci da ke Kwana Huɗu ya bayar da umarnin a yi wa Murja gwajin kwakwalwa.

Mai Shari’a Nura Yusuf ya ba da umarnin yi wa Murja gwajin kwakwalwar ne a asibitin gwamnati domin tabbatar da ƙoshin lafiyarta

Alkalin ya ba da umarnin ne bisa zargin jarumar ba ta cikin hayyacinta a lokacin zaman kotun na farko da aka gurfanar da ita.

Tun farko dai Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ce ta gurfanar da Murja kan zargin tayar da hankalin jama’a, bata tarbiyya da kuma koyar da karuwanci.

Dole talauci ya yi katutu a Arewa!

Hauhawar farashin kayayyaki ta ƙaru da kaso 33 a Najeriya — NBS

Kotun Ƙoli ta yi watsi da buƙatar rushe Hukumar EFCC

HOTUNA: Jana’izar tsohon Babban Hafsan Sojin Ƙasa Lagbaja