Kotu ta hukunta masu fyade da bulala 6 a Katsina
Wata Kotun Majistare ta yanke wa wasu mutum 4 hukuncin bulala shida kowannensu saboda kama su da laifin boye kananan mata biyu da yi masu fyade a Katsina. Wadanda aka hukuntan sun hada da Ahmed Lawal da Abdulmalik Mustapha da Adamu Khalid da Abubakar Lawal, dukkansu da ke zaune a Unguwar Rafukka, cikin birnin Katsina. […]
Wata Kotun Majistare ta yanke wa wasu mutum 4 hukuncin bulala shida kowannensu saboda kama su da laifin boye kananan mata biyu da yi masu fyade a Katsina.
Wadanda aka hukuntan sun hada da Ahmed Lawal da Abdulmalik Mustapha da Adamu Khalid da Abubakar Lawal, dukkansu da ke zaune a Unguwar Rafukka, cikin birnin Katsina. Dukkansu an tuhume su ne da cewa a ranar 20 ga Disamba, 2017 sun hada baki suka sace yaran mata biyu daga Unguwar Abbatuwa Katsina, suka kai su wani boyayyen wuri, suka yi masu fyade.
A lokacin da take yanke wannan hukunci, Majistare Fadila Dikko ta ce kotunta ta yi la’akari da cewa wannan shi ne karon farko da masu laifin suka aikata irin haka, don haka suka roki a yi masu sassauci, kuma kotun ta yi masu hukunci mai sauki.
Baya ga bulala shida-shida da za a yi wa kowannensu, haka kuma an yanke masu hukuncin daurin wata biyar a gidan yari ko kuma su biya tarar Naira dubu 2 kowannensu, sannan kuma su biya tarar Naira dubu biyar-biyar saboda laifin boye kananan matan da suka yi.