Kotu ta jingine hukunci a shari’ar kuɗin ƙananan hukumomin Kano
Babbar Kotun Jihar Kano ta jingine yanke hukunci kan kan ƙarar da aka gabatar mata da ke ƙalubalantar riƙe kuɗin ƙananan hukumomin jihar. Ƙungiyar Ma’aikatan Ƙananan Hukumomi ta Ƙasa NULGE ce dai ta shigar da ƙarar tana ƙalubalantar Babban Bankin Najeriya CBN kan riƙe wa ƙananan hukumomin jihar kuɗaɗensu. Isra’ila ta tsagaita wuta a Lebanon […]
Babbar Kotun Jihar Kano ta jingine yanke hukunci kan kan ƙarar da aka gabatar mata da ke ƙalubalantar riƙe kuɗin ƙananan hukumomin jihar.
Ƙungiyar Ma’aikatan Ƙananan Hukumomi ta Ƙasa NULGE ce dai ta shigar da ƙarar tana ƙalubalantar Babban Bankin Najeriya CBN kan riƙe wa ƙananan hukumomin jihar kuɗaɗensu.
Jagoran masu gabatar da ƙarar kuma Shugaban NULGE, Ibrahim Muhammad ya nemi kotun da ta hana CBN, Akanta-Janar na Tarayya riƙe kuɗin ƙananan hukumomi 44 na Jihar Kano.
Sai dai bayan sauraron lauyoyin kowane ɓangare, Mai shari’a Ibrahim Musa Muhammad ya ɗage ci gaba da sauraron ƙarar zuwa ranar da ya ce za a sanar da ɓangarorin da lamarin ya shafa.
Tun a farkon watan nan na Nuwamba ne Babbar Kotun Jihar Kano ta hana Babban Bankin Nijeriya (CBN) da Gwmanatin Tarayya riƙe kuɗaɗen ƙananan hukumomin jihar 44 na wata-wata.
Kotun ta bayar da umarnin wucin gadin ne ga Gwamantin Tarayya da hukumomi da ma’aikatunta, bayan ƙarar da Ƙungiyar Ma’aikatan Ƙananan Hukumomi ta Nijeriya (NULGE) da wasu masu kishin Jihar Kano suka gabatar.
Alƙalin kotun, Mai Shari’a Ibrahim Musa Muhammad, ya ba da umarnin ne ga CBN da Hukumar Rabon Kuɗaɗen Shiga ta Kasa da kuma Akanta-Janar na Tarayya kan taɓawa, riƙewa ko jinkirin sakin kuɗaɗen ƙananan hukumomin na Jihar Kano.
Alƙalin ya kuma umarci hukukumomin gwamantin da wakilansu da kada su kuskura su yi duk wani nau’in katsalandan kan kuɗaɗen ƙananan hukumomin.