Kotu ta kashe auren miji mai zagin matarsa

Kotun Kwastomari da ke zama a garin Ibadan na jihar Oyo ta raba aurenta wasu ma’auraa na shekara 20 saboda mijin ya kamanta matarsa da Alade. Oluwayemisi Ajakaye, wadda ke da ‘ya’ya uku tare mijinta ta bukaci kotu ta raban aurensu saboda a cewarta, “Mijina ya kuma kira na da akuya, karuwa, yana kuma bugu […]

Kotu ta kashe auren miji mai zagin matarsa

Ma’aurata

Kotun Kwastomari da ke zama a garin Ibadan na jihar Oyo ta raba aurenta wasu ma’auraa na shekara 20 saboda mijin ya kamanta matarsa da Alade.

Oluwayemisi Ajakaye, wadda ke da ‘ya’ya uku tare mijinta ta bukaci kotu ta raban aurensu saboda a cewarta, “Mijina ya kuma kira na da akuya, karuwa, yana kuma bugu na, ina da tabo daban-daban da zan iya nuna wa kotu”.

Ta ce, mijin nata yana kuma zarginta da bin maza, “har cewa ya ke ina kwanciya da kannena da makwabta kai har da fastonmu”.

Ta kuma ce ya gaya wa mahaifiyarta a waya cewar sai a gabanta zai kashe ta.

Sai dai kuma mijin nata, bai zo kotun don kare kansa ba, kuma bai turo wakilinshi ba.

Muhtin kotun kuma ya ce sau uku yana ba wanda ake zargin takardar gayyatar zaman kotu.

Mai Shari’a Ademola Odunade, da ke jagorantar sauran alkalai masu sauraron shari’ar ya raba auren kamar yadda Ajakaye ta bukata.

Mai Shari’a Odunade ya kuma damka mata kulawa da yaran su uku, shi kuma mijin ya rika ba ta N15,000 a duk wata don kulawa da su, kamar yadda kamfanin dillancin labarai ya ruwaito.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Tags