Kotu ta kashe aurensa kan yawan shan giya

Wata kotu ta raba auren wadansu ma’aurata, Toye Damilare da matarsa Tinuke Damilare bayan da mijin ya amsa laifin da ake zarginsa na yawan shan giya tare da lakada wa matar duka. Ya amsa laifin ne a gaban Kotun Gargajiya ta Oja-Oba da Mapo da ke Ibadan a inda matar tasa ta shigar da kara […]

Kotu ta kashe aurensa kan yawan shan giya
Kotu ta kashe aurensa kan yawan shan giya

Wata kotu ta raba auren wadansu ma’aurata, Toye Damilare da matarsa Tinuke Damilare bayan da mijin ya amsa laifin da ake zarginsa na yawan shan giya tare da lakada wa matar duka.

Ya amsa laifin ne a gaban Kotun Gargajiya ta Oja-Oba da Mapo da ke Ibadan a inda matar tasa ta shigar da kara tana neman kotun ta raba aurensu bisa dalilan shan giya da yake yi a kowane lokaci da kasa biyan bashin Naira miliyan 1 da ta ranto domin bunkasa harkokin kasuwancinsa.

Da take shaida wa kotun dalilan da  take so a raba auren, Tinuke Damilare ta ce “Ina jin takaicin zaman shekara 6 da wannan mutum da zai iya shanye jarka guda ta giya a rana  ba tare da tunawa da halin gidansa ke ciki ba.” Ta ce a kullum yana cikin shan giya ba dare ba rana, kuma idan ya shawo giyar ya dawo gida a buge sai ya huce a kanta da bugu. “Na baya-baya da ya aikata shi ne wanda ya kai ga kumbura min fuska da aman jini da na rika yi,” inji ta.

“Na sha kai kararsa ga iyayensa a kan wannan matsala da kuma ta rashin haihuwa amma suka yi biris ba tare da daukar matakin gyara ba, suna goyon bayansa a kan dukan abubuwan da suke aukuwa a tsakanina da shi. Sau biyu ina karbo bashin Naira dubu 500 daga banki domin bunkasa harkokin kasuwancinsa amma ya kasa biyan ko kwabo daga ciki,” inji ta

Ta ce ta fada cikin mawuyacin hali a yanzu saboda babu komai a hannunta da za ta iya juyawa. Ta ce ta sayar da kadarorinta domin biyan wannan bashi.

Da yake kare kansa mijin ya ce, “Gaskiyarta daya a kan batun shan giya, hakika ina shan giya, kuma ta sani sarai ina shan giya kafin ta aure ni. Amma ban taba dukanta ba. Na amince tana ranto kudi a madadina amma ina mayar mata da abin da ya sauwaka. Ita ce da kanta ta fice daga cikin gidan da muke zaune ban kore ta ba.”

Bayan sauraron bayanan miji da matar, Alkalin Kotun Cif Ademola Odunade ya raba auren nasu tare da umartar Toye ya kyale Tinuke ta kwashe dukan kayanta daga cikin gidansa.