Kotu ta ki bayar da belin El-Rufai
Magoya bayan El-Rufai sun fashe da kuka bayan kotu ta yi watsi da bukatar belinsa tare da dage sauraron shari’ar zuwa watan Yuni
Nasir El-Rufai, Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna
Babbar Kotun Jihar Kaduna ta yi watsi da bukatar belin tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, a ci gaban shari’ar da gwamnatin jihar ke tuhumar sa da almundahanar biliyoyin kudade da kuma amfani da mukami ta hanyar da ba ta dace ba.
Magoya bayan tsohon gwamnan sun fashe da bayan alkalin da ke jagorantar shari’ar, Mai Shari’a Darius Khobo, ya dage shari’ar tsohon gwamnan jihar, Nasir Ahmad El-Rufai, zuwa makon farko na watan Yunin 2026 domin fara sauraro.
Alkalin ya bayyana cewa bayan sauraron muhawarar vangarorin biyu, inda ake sa ran za a ci gaba da shari’ar kullum a zaman na gaba
Da yake magana da ’yan jarida jim kaxan bayan zaman kotun, wanda aka hana ’yan jarida shiga cikin kotun, lauyan El-Rufai, Ubong Akpan (SAN), ya nuna rashin jin daxinsa kan matakin kotun na qin bayar da beli tsohon gwamnan.
- Maniyyata aikin Hajji 2 daga Kano sun rasu a hatsarin mota
- Juyin mulki: Gwamnati ta maka waɗanda ake zargi a kotu
Ya ce, “Kotun cikin hikimarta ta yanke cewa saboda Nasir El-Rufai tsohon gwamna ne, hakan na nufin zai iya tsoma baki a bincike. Saboda haka ba shi da haqqin samun beli a cikin zargin almundahanar kuxi. Muna godiya ga Mai Shari’a kan ilimin da ya nuna, amma cikin girmamawa ba mu yarda ba. Faqat.”
Akpan ya qara da cewa, tawagar lauyoyin kare El-Rufai za su qalubalanci hukuncin ta hanyoyin shari’a da suka dace.
“An dage shari’ar zuwa makon farko na watan Yuni, kuma za a riqa sauraron ta kullum domin duba duk abin da ke cikin kundin shari’ar,” in ji shi, yana mai zargin cewa shari’ar da ake yi wa tsohon gwamnan tana da nasaba da siyasa.
Zargin siyasa a Shari’ar El-Rufai
“Tun daga farko, duk abin da ya shafi wahalhalun Nasir El-Rufai yana da alaqa da siyasa. Wannan kawai vangaren shari’a ne. Za mu fuskanci duk abin da ya zo,” in ji shi.
Dangane da takardun masu gabatar da qara, babban lauyan ya ce, “Takardunsu ba su xauke da siyasa a rubuce. Takardun shari’a ne. Don haka za mu mayar da martani gare su. Wannan shi ne abin da doka ta buqata mu yi.”
Tun da farko, Akpan ya yi jawabi ga magoya bayan El-Rufai a harabar kotu, inda da dama daga cikinsu sun nuna damuwa sosai, wasu ma suna zubar da hawaye kan wannan lamari.
“Dukkanku kuna nuna hali kamar wani ya mutu. Babu wanda ya mutu. Wani lokaci abubuwa na iya faruwa a rikici, amma kada ku ji tsoro. Ku tashi tsaye. Za mu ci gaba da wannan gwagwarmaya kuma za mu yi nasara,” in ji shi, yana kira gare su da su kwantar da hankalinsu.
Wakilinmu ya lura cewa da dama daga cikin magoya bayan sun nuna alamun damuwa bayan xage shari’ar.
Kimnain kwana 62 ke nan El-Rufai ke tsare a hannun hukuma, tun a ranar 18 ga watan Fabrairu, 2026, in banda kwana uku da aka sake shi bayan rasuwar mahaifiyarsa daga ranar 27 zuwa 31 ga watan Maris, 2026.
Zargin da ake wa El-Rufai
Hukumar Yaxi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) ce ta gurfanar da El-Rufai a gaban kotu bisa tuhume-tuhume guda tara da suka shafi zargin cin zarafin muqami, zamba da sauran laifukan kuxi.
Tuhume-tuhumen sun hada da zargin cewa ya sa gwamnatin jihar Kaduna ta fitar da kusan Naira biliyan 11 ga wata kungiya da ba a yi mata rijista ba domin aikin layin dogo na cikin gari wanda ba a aiwatar da shi ba.
Ana kuma zargin sa da amincewa da karvar kusan Naira miliyan 289.8 a matsayin kuxin sallama daga aiki fiye da adadin da doka ta tanada, da kuma karkatar da sama da Dala miliyan 1.08 daga rancen Bankin Duniya.
Sauran zarge-zargen sun haxa da bayar da kwangilar kyamarar tsaro ta CCTV ta Naira biliyan 4.6 ba bisa qa’ida ba, cin badaqalar filaye, da kuma yunqurin lalata bincike.
El-Rufai ya musanta dukkan zarge-zargen.